Radda Ya Yaye Jami’an Tsaron Daji 1,008 a Katsina, Ya Fadi Aikin da za Su Yi
- Gwamna Dikko Radda ya ce gwamnatin tarayya ta dauki matakan shawo kan matsalar tsaro a Katsina bayan ya nemi daukin Shugaba Bola Tinubu
- Ya bayyana cewa jami’an tsaron da aka horar za su taimaka wajen kare al’ummomi da dazuzzuka daga ayyukan ’yan bindiga.
- Radda ya ce an samu saukin matsalar tsaro, inda kasuwanni ke budewa, makarantu ke komawa aiki, manoma kuma ke komawa gonakinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa an kammala horas da jami’an tsaron daji 1,008, ciki har da mata 18, domin taimakawa wajen magance matsalar tsaro a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a bikin kammala horon jami’an, inda ya ce za su hada kai da sauran hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Gwamna Radda ya ce yana fatan hakan zai taimaka wajen kara inganta tsaron jihar Katsina.
Yadda Radda ya nemi taimakon Tinubu
Radda ya ce watanni kadan da suka gabata, lokacin da matsalar tsaro ta tsananta a yankunan Musawa da Matazu, ya kai ziyara ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin neman daukin gaggawa.
Ya ce shugaban kasar ya amsa bukatarsa ta hanyar kara ayyukan soji a yankunan da abin ya shafa da sauran sassan Katsina, tare da daukar jami’an tsaron daji sama da 1,000.
A cewarsa, wannan mataki ya taimaka wajen karfafa kokarin hukumomin tsaron da ke aiki a jihar.
Me jami’an tsaron daji za su yi?
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta samar wa jami’an da suka kammala horon kayan aiki da sauran tallafin da suke bukata domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwarsu da sauran hukumomin tsaro, musamman Rundunar Tsaron Al’umma ta Katsina.

Kara karanta wannan
Abin da ake zargi ya tabbata, jagoran ƴan bindiga ya faɗi dalilansu na ɗaukar makami
Radda ya bukaci jami’an da su kasance masu ladabi, kwarewa, biyayya da kuma mutunta hakkin dan Adam yayin gudanar da ayyukansu.
Magana kan halin tsaro a Katsina
Gwamnan ya ce ana samun saukin matsalar tsaro a hankali, inda kasuwanni ke sake budewa, makarantu ke komawa karatu, manoma kuma ke komawa gonakinsu.
Ya kara da cewa a halin yanzu, babu wata hanya a jihar Katsina da aka rufe saboda matsalar tsaro.

Source: Facebook
Radda ya gode wa Shugaba Tinubu bisa daukin da ya bayar, sannan ya yaba wa hukumomin tsaro, musamman Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (ONSA), bisa kokarinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da kokarin kwato dazuzzuka daga hannun masu aikata laifuka tare da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
An kashe 'yan bindiga a Katsina
A wani labarin, kun ji cewa rahotanni sun ce dakarun sojin Najeriya sun kashe akalla mutum 14 da ake zargin ’yan bindiga ne a wani artabu da ya faru a Gora.

Kara karanta wannan
An yi arangama da 'yan daba suka kai hari wurin taron magoya bayan Obi da Kwankwaso
Sojojin sun kuma kwato babura bakwai da ake zargin ’yan bindigar ke amfani da su wajen kai hare-hare a yankunan da suke gudanar da ayyukansu.
Nasarar da dakarun suka samu ta zo ne bayan rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun shirya wani mummunan shiri a kansu.
Asali: Legit.ng
