Kamfanin BUA Ya Tashi da Ribar kusan Rabin Naira Tiriliyan a cikin Watanni 9
- Daga Junairu zuwa Satumban shekarar nan ta 2026, kamfanin BUA ya samu ribar $339m a Najeriya
- Abdul Samad Rabiu mutumin Kano mai shekaru 66, shi ne wanda ya kafa kamfanonin BUA Group
- Babban kamfanin yana harkokin siminti, sukari, fulawa, taliyar abinci dakuma gine-gine a fadin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Lagos - Kamfanin simintin BUA Cement, mallakin hamshaƙin attajirin Najeriya, Abdul Samad Rabiu yana ta samun alheri a bana.
Kamfanin BUA ya samu ƙarin ribar 60% a cikin watanni tara na farkon shekarar 2026 sannan kuɗin da yake samu ya karu a lokacin.

Source: Facebook
Ribar simintin BUA ya wuce $300m
Kuɗin shigar kamfanin ya haura Naira tiriliyan ɗaya a shekarar nan. An samu wannan bayani ne a cikin rahoton Billionaires Africa.
A cewar rahoton kuɗin kamfanin da aka gabatar wa kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya, BUA ya samu riba sosai a kwanain nan.
BUA Cement ya samu ribar Naira biliyan 463.1 (dala miliyan 339) bayan cire haraji daga farkon Junairu zuwa 30 ga Satumba, 2026.
Wannan ya nuna ƙaruwar riba daga Naira biliyan 289.9 da kamfanin ya samu a makamancin wannan lokacin a shekarar da ta wuce.
N1.0tr ya shigo hannun kamfanin BUA
Kuɗin shigar kamfanin ya ƙaru da 26.5%, ya kai Naira tiriliyan 1.09 (dala miliyan 796).
Sai dai kuɗin da kamfanin ya kashe wajen samar da kayayyaki sun ƙaru da 8.8%, ana lisafin wannan karo ya kashe Naira biliyan 466.4.
Ribar da kamfanin ya samu kafin cire kuɗin gudanarwa da sauran abubuwa ta ƙaru da 44% domin ya yi hidimar fiye da Naira biliyan 600.
Haka kuma, ribar gudanar da harkokin kamfanin ta ƙaru da sama da 46% a yanzu.
Rahoton ya ce ribar da ake samu kan kowane kaso na hannun jari daga kamfanin simintin ya ta tashi daga N8.56 zuwa N13.68 a lokacin.
An samu raguwar ribar a zango na 3
Duk da samun gagarumar riba a cikin watanni taran nan, an samu raguwar saurin bunƙasar ribar kamfanin a zangon uku na shekarar.
A wannan zangon, ribar da kamfanin ya samu bayan haraji ta ƙaru da 26.9% (dala miliyan 101).
Kuɗin shigar kamfanin kuma sun kai Naira biliyan 357.8, wanda ke nuna an samu ƙaruwa da 28% a Yuli, Agusta da Satumban 2026.
Ribar kamfanin kafin cire haraji ta ƙaru da kashi 39.2 cikin 100, zuwa Naira biliyan 172.3. Sai dai kuɗin harajin da ya biya ya tashi.
Harajin da hukumomi suka karba hannun BUA ya nunka har ya kara, ya kai Naira biliyan 34.1.
Sannu a hankali yayin da watanni suke tafiya a shekarar 2026, ribar kamfanin simintin BUA yana ta raguwa daga Junairu zuwa yanzu.
Kamfanin ya samu Naira biliyan 176.4 a zangon farko, Naira biliyan 148.5 a zangon biyu, kafin ribar ta koma Naira biliyan 138.2.
Tasirin dala da raguwar ruwa a bashin kuɗi
Raguwar kuɗin da kamfanin ya samu yana da nsaba da canjin darajar kuɗin ƙasashen waje.
Sai dai raguwar kuɗin ruwa da ake biya kan basussuka ta taimaka wajen ƙara yawan ribar kamfanin a cikin watanni taran bana.
An kuma fahimci kuɗin ruwa da kamfanin ke biya sun ragu da 36.7 cikin 100, zuwa Naira biliyan 35.5.
Kuɗin ruwa da kamfanin ya samu daga ajiyarsa a bankuna sun kusan ninku sau uku, inda suka kai Naira biliyan 26.6 a yanzu.

Source: Facebook
Hannatu Musawa ta ziyarci Abdul Samad Rabiu
Rahoton nan ya ce Minista Hannatu Musawa ta kai ziyarar bazata ga tsohon mijinta, attajiri Abdul Samad Rabiu, a ofishinsa a Abuja.
Ziyarar ta jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka roƙi Rabiu ya sake aurenta idan dai akwai damar.
Dukansu sun nuna cewa har yanzu suna girmama juna duk da rabuwarsu, hakan yana burge jama'a.
Asali: Legit.ng


