Shugaban Kasa Bola Tinubu Zai Tafi Makkah domin Yi wa Najeriya Addu’a

Shugaban Kasa Bola Tinubu Zai Tafi Makkah domin Yi wa Najeriya Addu’a

  • Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai yi tafiya zuwa kasar Saudi gobe inda zai yi Umrah a birnin Makkah
  • Babban hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba
  • Cif Onanuga ya yi bayanin lokacin da shugaban kasar zai dawo da abubuwan da zai yi a kasa mai tsarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a ranar Alhamis zuwa Makka da ke ƙasar Saudiyya

Mai girma shugban kasa zai yi wannan tafiya ta musamman domin gudanar da Umrah, ibadar da Musulmi ke yi a Harami.

Shugaban kasa Bola Tinubu
Mai girma Bola Tinubu da dogarinsa a China Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bola Tinubu zai tafi birnin Makkah

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga ya fitar da wannan sanarwa a kafar X.

Hadimin shugaban Najeriyan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba 2027.

Kara karanta wannan

Matasa sun kira sarki a waya, sun yi barazanar yin garkuwa da shi a Kano

Bayo Onanuga ya ce ziyarar za ta ba Tinubu damar gudanar da ibada da kuma yin addu’o’in neman zaman lafiya ga ƙasarsa.

Baya ga haka zai yi addu’ar haɗin kai, kwanciyar hankali da ci gaba a lokacin da ake fuskantar babban zabe a Najeriya.

Ya bayyana cewa yayin da yake Makkah, shugaban ƙasar zai yi Umrah tare da neman shiriya da albarkar Ubangiji SWT.

Shugaban kasa zai ƙaddamar da kayan aikin sojoji

Kafin ya bar Birnin Abuja, ana sa ran Tinubu zai ƙaddamar da wasu kayan aiki da rundunar sojojin saman Najeriya ta saya.

Za a gudanar da bikin ƙaddamar da kayan aikin a ɓangaren filin jirgin Nnamdi Azikiwe da aka tanada domin shugaban ƙasa.

Ana sa ran shugaba Bola Tinubu zai dawo Najeriya a mako mai zuwa bayan kammala wannan ibada mai daraja a Musulunci.

Cikakkiyar sanarwar Fadar shugaban kasa

Ga sanarwar da aka samu daga shafin Mataimakin na shugaban kasa a yammacin Laraba.

TINUBU ZAI TAFI MAKKA DOMIN YI WA ƘASA ADDU’A
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a ranar Alhamis zuwa Makka da ke ƙasar Saudiyya, domin gudanar da ibadar Umara.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa Tinubu zafafan tambayoyi kan ciwo bashin $20bn da £1bn

Wannan ziyara za ta ba shugaban ƙasar damar keɓewa domin ibada, tunani da kuma yin addu’o’in neman zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa ga Najeriya.
Yayin da yake Makka, Shugaba Tinubu zai gudanar da ibadun da suka shafi Umara, tare da roƙon Allah Ya shiryar da Najeriya, Ya kuma albarkaci ƙasar da al’ummarta.
Kafin ya bar Abuja, Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da wasu kayan aiki da rundunar sojin saman Najeriya ta saya domin gudanar da ayyukanta. Za a gudanar da bikin ƙaddamar da kayan aikin ne a ɓangaren filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da aka tanada domin shugaban ƙasa.
Ana sa ran shugaban ƙasar zai dawo Najeriya a mako mai zuwa, bayan kammala ibadar.

- Bayo Onanuga

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara ta musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa.

28 ga Oktoba, 2026

Bashin Najeriya yana iya kai N200tr

Da zarar Bola Ahmed Tinubu ya samu yadda yake so, kun ji labari cewa bashin da ake bin Najeriya zai karu da N30tr.

Karin bashin yana nufin kudin da ake bin Gwamnatin tarayyar Najeriya zai zama saura kiris ya kai Naira tiriliyan 200.

Lissafi ya nuna akwai yiwuwar ya kasance ana bin duk ‘dan Najeriya har da na goye N830, 000 idan aka karo wasu kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng