Da Gaske Tinubu Zai Tafi Saudiyya domin Neman Maganin Rashin Lafiya? Bayanai Sun Fito

Da Gaske Tinubu Zai Tafi Saudiyya domin Neman Maganin Rashin Lafiya? Bayanai Sun Fito

  • Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan kafafen sada zumunta ya musanta zargin cewa shugaban ƙasar zai Saudiyya domin neman magani
  • Dada Olusegun ya ce Tinubu zai yi Umara tare da yi wa Najeriya addu’ar samun nasara da kuma sake zaɓensa a 2027
  • Ya bayyana cewa Tinubu ya je Makka domin yin Umara sau biyu a shekarar 2022, kafin zaɓen fitar da gwani na APC da zaɓen shugaban ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Dada Olusegun, mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan kafafen sada zumunta, ya musanta zargi cewa shugaban kasa zai je kasar Saudiyya ne domin a duba lafiyarsa.

Olusegun bayyana cewa shugaban ƙasar Bola Tinubu zai tafi Saudiyya ne domin gudanar da ƙaramin aikin Hajji, wato Umara, ba wai neman magani ba.

Kara karanta wannan

Magana ta fara fitowa, an ji dalilin da ya sa Tinubu ke son karbo bashin kusan Naira tiriliyan 30

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taro a fadar Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Abin da zai kai Tinubu Saudiyya

Hadimin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a ranar Alhamis, yayin mayar da martani ga wani saƙo da mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Omoyele Sowore, ya wallafa.

Olusegun ya kuma ce Tinubu zai yi amfani da damar wajen yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba, tare da roƙon Allah Ya ba shi nasarar sake zaɓensa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sowore ya yi zargin rashin lafiya

A saƙon da ya wallafa a ranar Laraba, Sowore ya ce Najeriya na cikin mawuyacin hali, yana mai cewa akwai alamun Tinubu zai sake yin wata tafiya zuwa ƙasar waje a ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026, a daidai lokacin da ake ƙara nuna shakku kan lafiyarsa.

Sowore ya kuma yi zargin cewa ana shirin tattara gwamnoni biyar, wasu ministoci da fitattun ’yan kasuwa domin raka shugaban ƙasar, da nufin nuna cewa tafiyar ta shafi harkokin gwamnati.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Bola Tinubu zai tafi Makkah domin yi wa Najeriya addu’a

Ya tambayi ko abin da ya faru da tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua na iya sake faruwa, yana mai cewa, “Kamar Yar’Adua, kamar Tinubu?”

Fadar shugaban ƙasa ta maida martani

Da yake mayar da martani ga zargin, Olusegun ya musanta cewa Tinubu zai tafi Saudiyya ns domin neman magani.

Ya ce shugaban ƙasar zai je ne domin yin Umara, kamar yadda sauran Musulmi a sassan duniya ke yi, tare da yin addu’o’i ga ƙasar da kuma miƙa batun sake tsayawarsa takara ga Allah.

A cewarsa, tafiyar ba sabon abu ba ce, domin Musulmi da dama kan yi addu’a yayin da suke shirin gudanar da muhimman al’amura a rayuwarsu.

Olusegun ya tunatar da Sowore cewa Tinubu ya je Makka, Saudiyya, domin yin Umara sau biyu a shekarar 2022.

Sowore.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AA kuma fitaccen dan gwagwarmaya a Najeriya, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Getty Images

Ya ce tafiyar farko ta kasance a watan Afrilu, kafin zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC, yayin da ta biyu ta kasance a ƙarshen watan Disamba, kafin zaɓen shugaban ƙasa.

Ya yi ikirarin cewa an amsa addu’o’in Shugaba Tinubu a waɗannan lokutan, yana mai cewa hakan ya sa shugaban ƙasar zai sake yin amfani da wannan hanya.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna Bafarawa ya kafa sharadin yi wa Tinubu kamfen a 2027

Atiku ya yi magana kan tafiyar Tinubu

Kun ji cewa Atiku Abubakar ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya rika fitar da hotuna da bidiyoyi a kullum domin tabbatar da cewa yana Makkah yana gudanar da ibadar Umrah.

Dan takarar shugaban kasa na ADC Atiku ya ce akwai dalilin zargin cewa Tinubu na iya yin ɗan gajeren zama a Makkah kafin ya wuce zuwa Faransa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262