"Ƙarfin Imanin Tinubu ga Allah SWT da Wasu Abubuwa 2 da Za Su Taimake Shi a Zaben 2027"

"Ƙarfin Imanin Tinubu ga Allah SWT da Wasu Abubuwa 2 da Za Su Taimake Shi a Zaben 2027"

  • Abdulaziz Yari ya ce dogaron Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga Allah SWT na daya daga cikin abubuwan da za su taimaka masa a zaben 2027
  • Tsohon gwamnan Zamfara ya yi magana ne a Makka, inda ya raka shugaban ƙasa da wasu fitattun ’yan Najeriya aikin Umara
  • Sanata Yari ya jaddada cewa APC-PCC zai yi ƙoƙarin gamsar da ’yan Najeriya domin su sake zaɓar Tinubu a wa’adi na biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Makkah, Saudi Arabia - Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC (APC-PCC), Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana dalilai uku da za su taimaki Shugaba Bola Tinubu.

Sanata Yari ya bayyana cewa wadannan abubuwa za su taimaka wa Shugaba Bola Tinubu samun ƙuri’un ’yan Najeriya a zaɓen shugaban ƙasa na watan Janairun 2027.

Kara karanta wannan

2027: Ɗiyar Tinubu ta yi maganar da ka iya tsorata 'yan Najeriya kan Atiku da Peter Obi

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da wasu yan tawagarsa da suka je Umrah a Makkah Hoto: Arewaforasiwaju
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Yari, tsohon gwamnan Jihar Zamfara, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida a ƙarshen mako a Makka, ƙasar Saudiyya.

Sanata Yari ya lissafo abubuwa 3

Abdulazizi Yari na cikin tawagar da ta raka shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da wasu fitattun ’yan Najeriya domin gudanar da aikin Umara. An samu faifan bidiyon hirar ne a ranar Asabar a Abuja.

Ya ce karfin imanin Tinubu ga Allah, ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar da kuma ƙarfin kwamitin yaƙin neman zaɓe wajen samun goyon bayan masu zaɓe su ne abubuwan da za su taimaka masa ya samu nasara a zabe mai zuwa

Yari ya kuma sake jaddada ƙudirin APC-PCC na ƙoƙarin samun goyon bayan ’yan Najeriya ga shirin Tinubu na neman wa’adi na biyu.

Tinubu ya nuna dogaro ga Allah

Jawabin Yari ya biyo bayan wata tattaunawa da manema labarai da Tinubu ya yi a Saudiyya ranar Juma’a, inda shugaban ƙasar ya bayyana irin jwarin gwiwa da yake da shi ga Allah kan sake zaɓensa.

Kara karanta wannan

Da gaske Tinubu zai tafi Saudiyya domin neman maganin rashin lafiya? Bayanai sun fito

Tinubu ya ce:

“Na yi imanin cewa abin da Allah Ya ƙaddara a wajenSa shi ne zai tabbata. Babu wpani abin bautawa da gaskiya sai Allah. Allah ne kaɗai zai iya ƙayyade makomar mutum, abin da zai zama da kuma abin da zai kasance a nan gaba.”

Yari ya ce wannan martani na shugaban ƙasa alama ce ta shugabanci na gari da kuma karfin imaninsa.

Sanata Yari.
Daraktan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Sanata Abdul'aziz Yari Hoto: Abdul'aziz Yari
Source: Facebook

Ya bayyana cewa lokacin da aka tambayi Tinubu, ya fara da yin addu’a ga ƙasar da kuma kowane ɗan Najeriya, sannan ya ce zaɓen shugaban ƙasa na hannun Allah ne, domin Shi ne kaɗai ke zaɓar wanda zai zama shugaba.

Tinubu ya yi Umrah a Saudiyya

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya gudanar da aikin Umrah da safiyar Juma’a da ta gabata a Masallacin Harami da ke Makkah, Saudiyya.

Shugaban ƙasar ya yi addu’ar godiya ga Allah Madaukakin Sarki tare da roƙonSa Ya ci gaba da shiryar da Najeriya, Ya kuma kare ƙasar da al’ummarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262