‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Malama Suna Neman Sai An Biya Naira Miliyan 50
- 'Yan bindiga sun yi garkuwa da malamar makarantar firamare, sun nemi fansar Naira miliyan 50 kafin a ske ta
- ‘Yan uwar malamar makaranta da aka sace a jihar Nasarawa sun roƙi jama’a da hukumomi su taimake su
- Masu garkuwa da mutanen sun buƙaci a biya su miliyoyi, ‘yanuwan Aminu Abdullahi ba su da wannan kudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Nasarawa - 'Yan bindiga sun sace Amina Hussaini, a gidanta da ke garin Kuru, ƙaramar hukumar Toto a Nasarawa ta Jihar Nasarawa.
Wannan baiwar Allah da aka yi garkuwa da ita, malamar firamare ce kuma kamar yadda aka ji, ana neman sai an biya su miliyoyin kudi.

Source: UGC
'Yan bindiga sun sace malamar makaranta
Daily Trust ta ce ‘yan bindigan sun nemi a biya su kuɗin fansa na Naira miliyan 50 kafin su saki wannan malama da ke hannunsu.
Wata ƴar uwarta, Suwaiba Abdullahi ce ta tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar ta wayar tarho a yammacin ranar Alhamis.
Ta ce an sace yaruwarta da take koyarwa a makarantar firamare ta LEA Primary School da ke Kuru, abin ya faru a ranar Talatar nan.
An yi awon gaba da malamar ne a lokacin da mijinta ya tafi birnin Lafia domin wani aiki.
Ana neman a biya fansar Naira milyan 50
A cewarta, masu garkuwar sun tuntubi iyalanta bayan sace ta, inda suka buƙaci a biya su Naira miliyan 50 kafin su fito masu da ta.
Suwaiba Abdullahi ta ce lamarin ya jefa danginsu cikin ruɗani, domin ba su san yadda za su tara irin waɗannan kuɗin masu yawa ba.
Ta ƙara da cewa wani ɗan uwa da ya shiga tsakani ya nemi a rage adadin kudin, amma ba a saurare shi ba.
Da wannan mutumi ya yi ƙoƙarin shawo kan masu garkuwa da mutanen su rage kuɗin fansar, sai suka katse wayar ana cikin tattaunawa.
'Yanuwa sun nemi taimakon gwamnati da jami'ai
Ƴar uwar malamar ta ce tuni iyalanta suka fara roƙon al'umma da su taimaka wajen ganin an kuɓutar da ita daga halin da ta ke ciki.
Ta ƙara da cewa har yanzu malamar tana hannun masu garkuwar, kuma sun kai rahoton lamarin ga rundunar ƴan sandan Nasarawa.
Suwaiba Abdullahi ta yi kira ga masu hannu da shuni, hukumomin tsaro da gwamnatin Nasarawa da su shiga cikin wannan lamari.
Suna roko su taimaka a saki ‘yaruwarsu cikin ƙoshin lafiya ba tare da an sanya masu wani sharadi ba.
'Yan bindiga sun fitini al'umma a yankin
Leadership ta ce wannan abu ya faru ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan matsalar tsaro a Toto da sauran sassan jihar.
A makon jiya, rundunar ƴan sandan jihar ta ƙaddamar da wani samame domin fatattakar ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel, ya ce shi ma ya ga rahotannin sace malamar a dandalin zumunta.
SP Ramhan Nansel ya ce zai gudanar da bincike kafin ya bayar da ƙarin bayani ga manema labarai.

Source: Getty Images
Kokarin jami'an kwastam a Legas
Labarin da aka samu shi ne hukumar Kwastam ta samu N6.2bn cikin awanni 24 a filin jirgin Murtala Muhammad da yake garin Legas.
Daga farkon shekara zuwa Oktoban 2026, sai da aka tara Naira biliyan 175 a reshen na filin jirgin.
ACG Godwin Otunla ya kuma bayyana tulin kwayoyi da kayan N118bn da suka karbe kuma an mika su ga shugabannin hukamar NDLEA.
Asali: Legit.ng


