'Yan bindiga sun sace mutane 16 a karamar hukumar Rafi

'Yan bindiga sun sace mutane 16 a karamar hukumar Rafi

Wasu 'yan bindiga sun dira karamar hukumar Rafi da ke jihar Neja tare da yin awon gaba da mutane 16 a kauyukan Magami da Tungan-Bako.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa 'yan bindigar sun dira kauyen a kan baura tare da fara yin harbin 'kan mai uwa da wabi'.

A cewar rahoton jaridar, 'yan bindigar sun yi awon gaba da mutane 8 a kauyen Magami tare da sake tafiya da wasun 6 a kauyen Tungan Bako.

Wata majiya ta bayyana cewa 'yan bindigar sun shiga gida - gida, inda suke fito da mutane tare da kwace musu kayayyakinsu masu muhimmanci.

Ibrahim Inga, babban darektan hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) reshen jihar Neja, ya tabbatar da faruwar kai harin.

Sai dai, bai bayar da wani karin bayani ba bayan tabbatar da cewa an kai harin da safiyar ranar Litinin.

A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng ta wallafa, a kalla mutane 19 rahotanni suka bayyana cewa sun rasa ransu sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai kauyen Kukum Daji a karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun sace mutane 16 a karamar hukumar Rafi
'Yan bindiga sun sace mutane 16 a karamar hukumar Rafi
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta rawaito cewa an kai harin ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Lahadi.

Kazalika, jaridar ta bayyana cewa wasu mutane 30 sun tsallake rijiya da baya bayan sun tsira da munanan raunuka.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun dira kauyen tare da yi wa mutane kisan gilla.

DUBA WANNAN: Nadin mukamai: Lauya ya shigar da karar Buhari a gaban kotu

Mista Yashen Titus, shugaban kungiyar cigaban kauyen Kukun Daji, ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa 'yan bindigar sun bude wuta a wurin wani taron biki da ake yi a wani gida a kauyen.

Ya kara da cewa 'yan bindiga sun dira kauyen da misalin karfe 10:35 na dare tare da fara yin harbin 'kan mai uwa da wabi'.

"Suna dauke da muggan makamai, mutane 17 daga cikin mutanen suka kashe sun mutu nan take a wurin da suka harbesu.

"An garzaya da mutane 32 zuwa asibiti domin ceton rayuwarsu, amma, abin takaici, biyu daga cikinsu sun mutu a asibiti.

"A yanzu haka da nake magana da ku, bamu san inda mazauna kauyen da dama suka shiga ba tun bayan da suka gudu daga gidajensu a lokacin da 'yan bindigar suka kawo hari.

"Mu na jin tsoron shiga jeji domin fara nemansu, saboda har yanzu ba a kawo jami'an tsaro yankin ba," a cewar Titus.

Kakakin jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da kai harin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel