An Farmaki Dan Takarar Shugaban Kasa a Wurin Cin Abinci a Najeriya, An Garzaya da Shi Asibiti

An Farmaki Dan Takarar Shugaban Kasa a Wurin Cin Abinci a Najeriya, An Garzaya da Shi Asibiti

  • Rundunar ’yan sandan jihar Ekiti ta tabbatar da cewa wasu mutane sun farmaki Omoyele Sowore, ɗan takarar shugaban ƙasa na AAC
  • An ruwaito cewa an farmaki Sowore har ya ji rauni yayin wata sa-in-sa da wasu mutane a wani gidan cin abinci
  • Kakakin rundunar ’yan sandan ya ce a halin yanzu ana duba lafiyar ɗan takarar a asibitin ’yan sanda da ke Ado-Ekiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ekiti, Nigeria – Rundunar ’yan sandan jihar Ekiti ta tabbatar cewa Omoyele Sowore, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, ya ji rauni yayin wata sa-in-sa da wasu mutane a wani gidan cin abinci.

Rundunar ta bayyana cewa mutanen da rigima ta hada su da dan gwagwarmayar sun farmake shi kuma a halin yanzu Sowore yana karɓar magani a wani asibiti da ke jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Halin da ɗalibai sama da 150 ke ciki bayan sun sha wani magani da ya masu illa a Katsina

Sowore.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Tun da farko, wani saƙo da aka wallafa a shafin Sowore na X ya nuna cewa wasu ’yan daba ɗauke da makamai sun yi awon gaba da shi a garin Ado-Ekiti, inda ba a san inda yake ba.

Da gaske an sace Omoyele Sowore?

Sai dai kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya ce ba a sace ɗan takarar shugaban ƙasar na AAC ba. Ya bayyana cewa a halin yanzu yana Asibitin ’Yan Sanda da ke Ado-Ekiti, inda ake duba lafiyarsa.

Abutu ya bayyana cewa jami’an tsaro sun samu rahoton cewa Sowore ya samu matsala da wasu mutane a wani gidan cin abinci da ke Ado-Ekiti a ranar Juma’a, inda suka garzaya wurin domin ceto shi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Ado-Ekiti ranar Juma’a, Abutu ya ce bayan ceto Sowore, an kai shi Asibitin ’Yan Sanda, inda a halin yanzu yake karɓar magani kan ƙaramin raunin da ya samu.

Kara karanta wannan

Jami'an gwamnatin Kano sun yi tattaki zuwa jihar Ribas, sun kamo wani mutumi da ake zargi

A rahoton Ounch, kakakin rundunar yan sanda ya ce:

“Kwamishinan ’yan sandan jihar, Michael Falade, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin sirri kan lamarin domin gano cikakken abin da ya haddasa sa-in-sar, gano dukkan mutanen da ke da hannu a ciki da kuma tabbatar da cewa an gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban shari’a.”

Yan sanda sun kwantar da hankali

Rundunar ’yan sandan ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu, tare da yin watsi da bayanan da ke yaɗawa na cewa an yi garkuwa da Sowore.

Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Ta kuma buƙaci jama’a da su guji yaɗa bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba, waɗanda ka iya haddasa fargaba da tashin hankali ba tare da wani dalili ba.

Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa, matsayi ko asalin mutum ba.

Yadda aka farmaki tawagar Sowore

Tun farko kun ji cewa an kai wa dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore hari a wani gidan cin abinci a jihar Ekiti, inda aka fara yada labarin cewa an yi garkuwa da shi.

Bayanan da aka samu sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wajen wani cin abinci da ke Ado-Ekiti da ranar Juma'a, 30 ga Oktoba 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262