'Yan Bindiga Sun Bi Gari Gari, Sun Kashe Bayin Allah tare da Sace Mutane Sama da 100

'Yan Bindiga Sun Bi Gari Gari, Sun Kashe Bayin Allah tare da Sace Mutane Sama da 100

  • Yan bindiga sun kai farmaki garuruwa da dama a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja, sun kashe mutum biyu tare da sace wasu 122 a wata ɗaya
  • Ɗan Majalisar dokokin jihar Neja mai wakiltar Rafi, Hon. Zubairu Isma'il Zannah ne ya bayyana hakan da yake gabatar da kudiri a Majalisa
  • Bayan tattaunawa kan lamarin, Majalisar ta bukaci gwamnatin Neja ta haɗa kai da gwamnatin Kaduna wajen kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Dan majalisar dokokin jihar Neja mai wakiltar mazabar Rafi, Zubairu Ismail Zannah, ya bayyana damuwarsa kan yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a yankin.

Ɗan majalisar ya ce ƴan bindiga na cin karensu babu babbaka a yankin, inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu 122 cikin wata guda kacal.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki masallaci, sun sace limami da masallata

Taswirar Neja.
Yan bindiga sun kashe mutane 2, sun sace wasu 122 a jihar Neja a wata ɗaya Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ɗan Majalisa ya koka da matsalar ƴan bindiga

Hon. Zubairu ya bayyana hakan ne da yake gabatar da kudiri a zauren Majalisar dokokin jihar da ke Minna, babban birnin Neja, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi ga sauran abokan aikinsa yayin gabatar da kudirin, Hon. Zubairu Isma'il ya ce garuruwan da ƴan bindigar suka fi matsawa lamba sun haɗa da Pandogari, Wowo, Gidigori, Ringa da Kawu.

Ya ce mutane da dama sun rasa matsugunansu yayin da ‘yan bindiga suka lalata gonakinsu da amfanin gona, lamarin da ke kara jefa su cikin matsin tattalin arziki.

Bayan gabatar da kudirin, nan take Hon. Abdulmalik Bala Yakubu mai wakiltar mazaɓar Katcha ya mara masa baya.

Majalisar Neja ta lalubo mafita kan matsalar

Daga nan Majalisar ta bukaci gwamnatin jihar Neja ta hada kai da gwamnatin Kaduna domin magance wannan matsala.

Majalisar dokokin ta lura cewa karuwar hare-haren ‘yan ta'adda a ƙananan hukumomin a Rafi, Munya, da Shiroro na da alaka da kokarin da gwamnatin Kaduna ke yi na fatattakar ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan rahoton tura bukatar ƙirƙirar jihohi 31, Majalisa ta fayyace komai

A cewar ƴan majalisar dokokin, hakan ya tilastawa miyagun ƴan ta'adda tserewa daga Kaduna suna kwarara cikin yankunan jihar Neja.

Ya kamata Kaduna da Neja su haɗa kai

Domin shawo kan matsalar, majalisar dokokin ta bukaci hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Neja da Kaduna don tunkarar ‘yan bindiga.

Sannan kuma ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara girke jami’an tsaro a yankunan da matsalar ta fi kamari.

Haka zalika Majalisar dokokin Neja ta yanke shawarar zaman tattaunawa da gwamnatin tarayya domin daukar kwararan matakai.

Matsalar ‘yan bindiga a Neja na kara kamari, musamman a yankunan da ke kusa da jihar Kaduna, lamarin da ke barazana ga rayuka, arziki da tsaron jama’a.

Masu haƙo ma'adanai sun mallaki makamai

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Neja, Muhammed Umar Bago ya koka kan yadda wasu masu haƙar ma'adanai suka mallaki bindigogi da nakiya.

Gwamnan, wanda ya kai ziyara wani kauye da nakiya ta tashi, ya ce wannan babbar barazana ce ga tsaro a daidai lokacin da ake fafutukar magance hare-haren ƴan bindiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262