Yadda Yar Chibok Ta Ki Amincewa da Iyayenta, Ta Nemi Bin Mijinta Dan Boko Haram

Yadda Yar Chibok Ta Ki Amincewa da Iyayenta, Ta Nemi Bin Mijinta Dan Boko Haram

  • Tsohon shugaban Hukumar Leƙen Asirin Ƙasa, Ahmed Rufai, ya bayyana yadda wata yarinyar Chibok da aka ceto ta nemi komawa wajen mijinta ɗan Boko Haram
  • Ya ce matar ta auri mayaƙan Boko Haram uku, inda aka kashe mazajenta biyu na farko yayin faɗa
  • Rufai ya bayyana cewa lamarin ya nuna wahalar sake shigar da waɗanda suka shafe shekaru a hannun ’yan ta’adda cikin al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon darakta-janar na Hukumar Leƙen Asirin Ƙasa (NIA), Ambasada Ahmed Rufai, ya tuna abin mamaki da ya faru kan matsalar Boko Haram.

Rufai ya bayyana yadda wata yarinyar Chibok da aka ceto ta nuna sha’awar komawa wajen mijinta ɗan Boko Haram.

Wata yar Chibok ta nuna sha'awar komawa ga mijinta dan Boko Haram
Tsohon shugaban NIA, Ahmed Rufai da Bola Tinubu. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Twitter

Rufai ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan ƙalubalen ceto waɗanda ta’addanci ya shafa da kuma sake shigar da su cikin al’umma.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Jigon APC ya yi wa Atiku tatas, ya bukaci ya yi ritaya daga siyasa

Ya yi wannan bayani ne a wani taron ƙasa da ƙasa kan tsaro da aka gudanar a ƙasar Qatar.

Yaushe aka sace yan matan Chibok?

A ranar 14 ga Afrilu, 2014, mayakan Boko Haram sun sace ɗalibai mata 276 daga makarantar sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke Chibok, jihar Borno.

Lamarin ya jawo Allah-wadai daga cikin gida da ƙasashen duniya, inda wasu daga cikin ɗaliban suka tsere ko aka sako su, yayin da wasu suka shafe shekaru a hannun ’yan ta’addan.

Wasu daga cikin ɗaliban kuma an tilasta musu aure da mayaƙan ƙungiyar, lamarin da ya ƙara rikitar da ƙoƙarin dawo da su cikin al’umma.

Yadda aka ceto ta bayan ta auri mayaƙa 3

Da yake ƙarin bayani, Rufai ya ce sace mutane da ƙungiyoyin ta’addanci ke yi yana da dalilai daban-daban, ciki har da akida, siyasa da neman kuɗi.

Ya ce waɗannan dalilai na buƙatar hukumomin tsaro su bi hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar da kuma ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Obi ya fadi yadda zai yi aiki tare da Kwankwaso idan suka yi nasara a 2027

Da yake ba da labarin yarinyar Chibok ɗin, tsohon shugaban leƙen asirin ya ce ta auri mayaƙan Boko Haram uku, amma an kashe mazajenta biyu na farko a fagen daga.

Daga bisani, jami’an tsaro sun kuɓutar da ita tare da kai ta Abuja, inda aka yi mata gwaje-gwajen lafiya da tambayoyi domin fahimtar halin da take ciki.

Ta nemi komawa wajen mijinta

Tsohon shugaban NIA ya ce abin da ya fi ba shi mamaki shi ne yadda matar ta nuna sha’awar komawa bayan an kuɓutar da ita.

Ya ce:

“Tana son iyayenta. Tana son ganinsu da sauran abubuwa. Abu na uku mai ban sha’awa shi ne, mun yi mata gwaje-gwajen lafiya kuma muka gano cewa tana cikin ƙoshin lafiya. Amma abin mamaki, tana son komawa.”

Rufai ya ce wannan lamari ya nuna irin rikitarwa da jami’an tsaro ke fuskanta wajen kula da waɗanda suka shafe shekaru a hannun ’yan ta’adda.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda aka sace kan ƙulla dangantaka da mutanen da suka yi garkuwa da su, wanda hakan ke sa komawa cikin al’umma ya zama babban ƙalubale.

Kara karanta wannan

Tafiyar Tinubu zuwa Makkah ta jawo masa abin da bai yi zato ba

Boko Haram ta yi wa gwamnati gargadi

Mun ba ku labarin cewa kungiyar Boko Haram ta bayar da wa’adin sa’o’i 72 tare da barazana kan mutane 416 da ta yi garkuwa da su a wani daji.

'Yan ta'addan sun yi barazanar rarraba su zuwa wurare daban-daban idan ba a biya bukatunta da ta zayyana wa gwamnati ba.

Boko Haram ta yi wa gwamnati taƙama, inda ta ƙalubalance ta a aiko dakaru sun zo su kwaci mutanen idan an isa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.