'Yan Sanda Sun Yi Magana kan Sace Dan Takarar Shugaban kasa, Sun Fadi Abin da Ya Faru
- ’Yan sanda sun ce ba a sace Omoyele Sowore ba, kamar yadda wani saƙo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna
- Sowore ya samu ƙaramin rauni bayan wata takaddama da wasu mutane a wani gidan cin abinci a yankin Dalimore, Ado-Ekiti
- Rundunar ta ce kwamishinan ’yan sanda ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin lamarin da waɗanda suka aikata laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ekiti - Rundunar ’yan sandan jihar Ekiti ta musanta rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an sace ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, a garin Ado-Ekiti.
Wani saƙo da aka yaɗa ya yi ikirarin cewa an yi garkuwa da Sowore kuma ba a san inda yake ba. Sai dai rundunar ta ce wannan labari ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan
An farmaki ɗan takarar shugaban ƙasa a wurin cin abinci a Najeriya, an garzaya da shi asibiti

Source: Twitter
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar a jihar, SP Sunday Abutu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar wadda Legit Hausa ta samu daga wajen shi.
Ya bayyana cewa bayanan farko sun nuna Sowore ya samu saɓani da wasu mutane a wani gidan cin abinci da ke yankin Dalimore a Ado-Ekiti.
Yadda lamarin ya faru
Abutu ya ce bayan samun rahoton abin da ya faru, jami’an ’yan sanda sun garzaya wurin lamarin, inda suka yi nasarar kuɓutar da Sowore.
Sai dai ya bayyana cewa ɗan siyasan ya samu ƙaramin rauni a yayin takaddamar, kuma a halin yanzu yana karɓar kulawar likitoci a asibitin ’yan sanda da ke Ado-Ekiti.
A kalamansa, jami’in ya ce:
“Duk da haka, ya samu ƙaramin rauni kuma a halin yanzu yana karɓar kulawar likitoci a Asibitin ’Yan Sanda da ke Ado-Ekiti.”
Kwamishinan ’yan sanda ya ba da umarni
Rundunar ta bayyana cewa kwamishinan ’yan sandan jihar Ekiti, CP Falade Adegoroye Michael, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin sirri domin gano cikakken abin da ya faru.
Binciken zai kuma taimaka wajen gano dukkan mutanen da suka shiga lamarin da kuma tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Rundunar ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da yin watsi da rahoton da ke cewa an sace Sowore.
Ta kuma buƙaci jama’a su guji yaɗa labaran da ba a tantance sahihancinsu ba, musamman waɗanda za su iya haddasa firgici da tashin hankali a tsakanin al’umma.
Da Legit Hausa ta tambaye shi kan zargin Sowore na cewa gwamnati ce ta dauki nauyin 'yan daban da suka farmake shi, kuma DSS ta sanar da su inda suke, sai kakakin ya ce ana ci gaba da bincike.
"Abin da kawai zan iya cewa kenan, ana ci gaba da bincike kan lamarin." In ji shi.
Dalilin ziyarar Sowore a jihar Ekiti
Sowore na jihar Ekiti ne domin halartar gasar gudun fanfalaki ta Ikogosi ta shekarar 2026, mai tsawon kilomita 17.5.
Ana sa ran gudanar da gasar ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026, inda za a fara daga Ilawe-Ekiti da ke ƙaramar hukumar Ekiti South West zuwa Ikogosi, a ƙaramar hukumar Ekiti West.

Source: Original
Sowore ya yi watsi da shirin hadaka
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi watsi da shirin shiga haɗakar jam’iyyun adawa.
Omoyele Sowore ya kuma yi hasashen cewa haɗakar za ta rushe bayan babban zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara.
Asali: Legit.ng

