Abin Tausayi: 'Yan Bindiga Sun Nuna wa Mata kusan 30 da Karamin Yaro Rashin Imani
- Wasu miyagun ’yan bindiga sun kai hari ƙauyuka huɗu a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja, inda suka sace mata 29 da karamin yaro
- Rahotanni sun ce jami’an tsaro na haɗin gwiwa, ƙarƙashin jagorancin ’yan sanda na Bangi, sun bi sawun maharan jim kaɗan bayan sace matan
- Rundunar ’yan sanda reshen jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin da kuma ceto wasu daga cikin matan da aka yi garkuwa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Wasu ’yan bindiga da ba a san daga inda suka fito ba sun kai hari ƙauyuka huɗu a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja a yankin Arewa ta Tsakiya.
Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun tattara mata 29 da wani karamin yaro, sun yi awon gaba da su da nufin komawa maboyarsu domin su yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan bindiga sun kai hari kusa da masallacin Juma'a na jami'ar Usman Danfodio

Source: Original
Yan bindiga sun shiga kauyuka 4 a Neja
Jaridar Leadership ta tattaro cewa maharan sun kai hare-haren ne a ƙauyukan Kwimo, Kalgo, Kakaki da Mabona duk a karkashin karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Bayanai daga mazauna yankin sun ce jami’an tsaro na haɗin gwiwa, ƙarƙashin jagorancin ’yan sanda na caji ofis din Bangi, sun bi sawun maharan jim kaɗan bayan faruwar lamarin.
Wani mazaunin yankin mai suna Mohammed Ibrahim ya shaida wa manema labarai cewa jami’an ’yan sanda sun yi nasarar bin sawun masu garkuwar tare da ceto wasu daga cikin waɗanda aka sace.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma ceto wasu daga cikin matan.
Tabbatarwar ta nuna cewa jami’an tsaro sun ɗauki matakai bayan faruwar harin, duk da cewa ba a bayyana ƙarin bayanai kan yadda aka gudanar da aikin ceton ba.
Haka kuma, ba a samu cikakken bayani kan lokacin da maharan suka kai harin ba, ko kuma ko sun tuntubi iyalan waɗanda aka sace domin neman kuɗin fansa.
Jami'an tsaro sun ceto mata 11
Harin ya sake jawo hankali kan matsalar tsaro da ke addabar wasu al'ummomi a jihar Neja, musamman a yankunan karkara.

Source: Twitter
Kakakin yan sandan ya bayyana cewa mata 11 daga cikin wadanda aka sace ns suka kubuta, yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da farautar maharan domin ceto sauran wadanda ke hannunsu.
SP Wasiu Abiodun ya ce:
"Bayan maharan sun yi yunkurin tafiya da mata 29 da karamin yaro, jami'an tsaro sun bi sahunsu, daga bisani mata 11 suka tsere suka dawo gida.
"A halin yanzu rundunar yan sanda na ci gaba da jagorantar aikin ceto domin kubutar da sauran wadanda suka rage."
Yan bindiga sun yi barna a Neja
Kun ji cewa ’yan bindiga sun kashe manoma biyar, sun sace mutane 18, tare da kona gidaje da shaguna a wasu kauyukan jihar Neja.
Hare-haren sun faru ne tsakanin 9 zuwa 12 ga Oktoba, 2026, a Fanga da ke ƙaramar hukumar Mashegu, da Kigbere da Kokani a ƙaramar hukumar Borgu.
Asali: Legit.ng
