Bayan Kama Ɗan Agajin Izala, Kiristocin Arewa Sun ba Ƴan Sanda Shawara
- Rabaran John Joseph Hayab ya bukaci ’yan sanda su kama duk wadanda ke da hannu a bidiyon barazanar kashe Kiristoci a Zamfara
- Hayab ya yaba wa ’yan sanda bisa kama wani wanda ake zargi, amma ya ce dole a binciki duk wadanda suka shiga lamarin ba tare da la’akari da addini ko kabila ba
- Shugaban Kiristocin ya bukaci Kiristoci kada su bari bidiyon ya tsorata su, yayin da ya yi kira ga shugabannin addinai su ci gaba da tattaunawa domin zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Shugaban kungiyar Kiristocin Arewa, Reverend John Joseph Hayab, ya yi magana kan cafke dan agajin Izala da aka yi.
Hayab ya bukaci ’yan sanda su kama tare da gurfanar da duk wadanda ke da hannu a wani bidiyo da ya yadu, wanda ake zargin wasu matasa sun yi barazanar kashe Kiristoci a Zamfara.

Source: Facebook
Da yake magana yayin wata hira da Arise News a ranar Alhamis, Hayab ya yaba wa ’yan sanda bisa kama matashin.
Abin shugaban Kiristocin Arewa ya ce
Hayab ya dage cewa dole ne duk wadanda ke da hannu a lamarin su fuskanci hukunci, ba tare da la’akari da addininsu ko kabilarsu ba.
Ya ce:
“Abu daya ne a kama shi. Abu daya ne a fito da shi a gaban jama’a. Amma bin dukkan matakan shari’a har sai an tabbatar da an yi adalci, wani abu ne daban”
Haka kuma, Hayab ya yaba wa kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) bisa mika wanda ake zargin ga ’yan sanda
Hayab ya bukaci ’yan sanda su binciki duk wadanda ake zargin sun shiga cikin shirya barazanar ko suka goyi bayanta, yana mai gargadin kada a kare wadanda ake zargi saboda addini ko yankin da suka fito
Ya ce:
“Idan ya cutar da Kiristoci a yau, to wata rana zai iya cutar da kai, duk da cewa kana tunanin dan uwanka ne”
Ya kuma yi tambaya kan ikirarin cewa an yi wa bidiyon magudi, yana mai cewa ana zargin wanda aka kama ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook kafin daga bisani ya cire shi

Source: Facebook
Hayab ya karfafawa Kiristoci guiwa
Shugaban Kiristocin ya bukaci Kiristoci a Arewacin Najeriya kada su bari bidiyon ya tsorata su ko ya hana su gudanar da addininsu, yana mai kira ga gwamnati da ta tabbatar an hukunta wadanda suka yi barazanar bisa doka
Ya kuma yi gargadi kan koyar da matasa akidun addini ta hanyar da za ta tunzura su, yana zargin wasu masu wa’azi da amfani da karancin ilimi wajen juya matasa kan mabiya sauran addinai
Hayab ya amince cewa wasu malaman addinin Musulunci sun yi Allah wadai da bidiyon, yana mai cewa shugabannin Kiristoci da Musulmi na tattaunawa domin warware korafe-korafen da ke tsakaninsu
Ya ce:
“Muna son tattauna abubuwan da ke bata wa Kiristoci rai game da Musulmi. Haka kuma, muna son tattauna abubuwan da ke bata wa Musulmi rai game da Kiristoci”
Ya bukaci shugabannin addinai su ci gaba da tattaunawa tare da karfafa mutunta juna, yana mai jaddada cewa ci gaban Najeriya ya dogara da zaman lafiya da kare hakkin kowane dan kasa.
Izala ta magantu kan bidiyon dan agaji
A baya, an ji cewa kungiyar Izala ta Najeriya ta yi Allah wadai da bidiyon wani matashi sanye da kayan agajjinta hana fadar kalaman tunzura jama'a.
Sheikh Bala Lau ya bukaci jami’an tsaro gudanar da bincike kan bidiyon dan agajin, wanda ke ta yada wa a kafafen sada zumunta.
Mutashin da ya bayyana a bidiyon yana neman a ba su bindigogin AK-47 domin su je Enugu da Joa ranar Lahadi su kai hari.
Asali: Legit.ng


