Kiristoci Sun Fusata da Fasto Ya Ce Ya Je Har Aljanna, Ya Ga Yesu Ido da Ido

Kiristoci Sun Fusata da Fasto Ya Ce Ya Je Har Aljanna, Ya Ga Yesu Ido da Ido

  • Ikirarin wani fasto Najeriya na ziyartar aljanna da ganin Yesu Almasihu ya jawo saɓani tsakanin shugabannin Kirista
  • Fasto Arome Osayi ya yi ikirarin cewa Yesu ya umarce shi da tura Naira miliyan biyar ga wani fasto bayan ya nemi ikon tayar da matattu
  • Wasu shugabannin Kirista sun yi gargaɗin cewa fastoci na iya ƙirƙirar labaran wahayi domin neman kuɗi da ƙarin mabiya, yayin da wasu suka kare yiwuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lagos - Kalaman fasto Arome Osayi na cewa ya ziyarci sama, sun ga Yesu Almasihu ido-da-ido ya jawo magana a tsakanin Kiristoci.

Faston ya ce ya karɓi umarni daga Ubangiji wanda ya raba kan shugabannin Kirista, inda wasu ke cewa ana iya ƙirƙirar irin waɗannan labarai domin samun mabiya da kuɗi.

Fasto ya jawo magana kan ikirarin zuwa aljanna
Fasto Arome Osayi da ya jawo maganganu kan ikirarin zuwa aljanna. Hoto: Apostle Arome Osayi.
Source: Instagram

Wasu shugabannin coci da suka tattauna da jaridar Punch sun dage cewa Allah na iya bayyana kansa ga mutane ta hanyar abubuwan da suka shafi ruhaniya.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya sake neman alfarmar yan Najeriya yayin kamfen a Kaduna

Maganar fasto da ta jawo ce-ce-ku-ce

Sai dai wasu sun ce ya kamata a binciki ikirarin abubuwan ban mamaki domin hana yaɗuwar koyarwar da za ta iya yaudarar mutane da cin moriyar masu ibada.

Rikicin ya biyo bayan yaɗuwar wasu bidiyoyi da suka nuna wanda ya kafa cocin Remnant Christian Network, fasto Arome Osayi, yana ba da labarin abubuwan ban mamaki da ya ce ya fuskanta tare da Yesu Almasihu.

A cikin ɗaya daga cikin bidiyoyin, Osayi ya yi ikirarin cewa Yesu ya bayyana gare shi, inda ya kwashe sa’o’i tara yana “kuka da ƙorafi” kan halin da cocin Najeriya ke ciki.

A cewar malamin addinin, Yesu ya nuna rashin jin daɗinsa saboda cocin ta gaza samar da sakamakon da ake tsammani, duk da jarin ruhaniya da aka zuba a cikinta.

A wani bidiyo kuma, malamin ya yi ikirarin cewa Yesu ya bayyana gare shi bayan ya nemi ikon tayar da matattu da kuma warkar da masu cutar Autism.

Kara karanta wannan

Siyasa na ɗaukar zafi, ƴan daba sun farmaki ɗan takarar majalisa, an rasa rai

A cewar Osayi, Yesu ya gaya masa ya tura Naira miliyan biyar ga wani fasto.

Osayi ya ce:

“Na ce, ‘Ba za ka ba ni ikon tayar da matattu da kuma ikon warkar da Autism ba?’ Ya ce, ‘Ka tura wa wancan faston miliyan biyar,’ sai na ce, ‘Na amince.’”
Labarin ya jawo suka daga wasu shugabannin Kirista, ciki har da wanda ya kafa cocin Power City International, Fasto Abel Damina, wanda ya bayyana ikirarin a matsayin “labaran ƙanzon kurege da tatsuniyoyi.”

Ya tambayi yadda labaran Osayi suka dace da juna, yana mai cewa ya kamata fastoci su yi taka-tsantsan wajen bayyana abubuwan ban mamaki da suka ce sun fuskanta.

Babban Fasto Apostle Johnson Suleman, shi ma ya nuna shakku kan ikirarin wasu fastoci na cewa sun ziyarci sama sau da dama.

A yayin wa’azi a wani bidiyo, Suleman ya nuna rashin yarda da labaran mutanen da ke cewa sun yi tafiya zuwa sama a lokuta da dama.

An taru wa fasto kan kalamansa
Fasto Arome Osayi da ya jawo magana a Najeriya. Hoto: Apostle Arome Osayi.
Source: Instagram

Wahayi ne ko ƙirƙirar labarai?

Kara karanta wannan

Yadda 'yunwa' za ta ruguza lissafin Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027

Da yake magana da manema labarai, shugaban Nigeria Council for Theological Studies and Christian Education, Farfesa Olowookere David, ya kare yiwuwar samun ganawa da Allah ta hanyar abubuwan ban mamaki.

Ya bayyana cewa Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi labaran wahayi daga Allah, kuma Allah na iya bayyana kansa ga mutane ta hanyoyi daban-daban.

Malamin addinin ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa fastocin da ke bayyana labaran ziyartar sama da ganawa da Yesu Almasihu suna raina Kiristanci.

Fasto ya magantu kan asalin sallar layya

A baya, mun ba ku labarin cewa fitaccen faston CAC a Najeriya ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya bayyana wasu sababbin bayanai game da sallar layya.

Faston ya ce Annabi Ishaqa da Isma’il ‘ya’yan Annabi Ibrahim ne da suka fi kusanci da Kiristoci, yana danganta hadayar Ishaqa da addinin Kirista.

An bayyana muhimmancin watan Zul-Hijja da bikin Ojude Oba a Ijebu-Ode, yayin da Musulmai ke shirin gudanar da bikin babbar salla.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.