Amurka ta Kawo Dauki Mai Zafi, Manyan Yan Ta'adda Sun Fara Guduwa a Najeriya
- Kwamandan AFRICOM ya ce yawan mayakan ISIS da ke fita adaga syyukan ta'addanci ya karu da sama da kashi 200% a Najeriya.
- Ya danganta karuwar da nasarar farmakin da aka kai kan wani babban jagoran kungiyar da sauran hare-haren sojojin Najeriya da na Amurka
- Ya ce tallafin soji kadai ba zai magance matsalolin tsaro a Najeriya ba, yana mai jaddada muhimmancin shugabanci nagari da ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Amurka ta bayyana cewa hadin gwiwarta da Najeriya ya fara tilasta wa mayakan ISISI guduwa tare da daina ayyukan ta'addanci a Najeriya.
Kwamandan rundunar sojin Amurka mai kula da Afirka (AFRICOM), Dagvin Anderson, ya ce yawan mayakan kungiyar ISIS da ke tuba a Najeriya ya karu da sama da kashi 200%.

Source: Getty Images
A rahoton The Cable, kwamandan ya ce mayakan ISIS na guduwa su bar ayyukan ta'sddanci tun bayan wani farmaki da sojojin Najeriya da Amurka suka gudanar tare a watan Mayu.

Kara karanta wannan
Bincike ya tono matsala a N37bn da aka ce gwamnatin Tinubu da Buhari sun raba wa talakawa
A cewar jaridar THISDAY, Anderson ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin wani taron baje kolin kayan aikin tsaro na kasa da kasa na Afirka (AFRIDEX), da aka gudanar a Legas.
Hadin gwiwar Amurka da Najeriya
Ya danganta karuwar mika wuya da tasirin farmakin da aka kai kan wani babban jigo a kungiyar ISIS, da kuma hare-haren soji da dakarun Najeriya suka ci gaba da gudanarwa bayan hakan.
Ya ce Amurka na ci gaba da hadin gwiwa da jami’an tsaron Najeriya ta hanyar samar da bayanan sirri, kwarewa ta musamman da horo.
Anderson ya ce:
“Hadakar da muka yi da rundunar sojin Najeriya da jami’an leken asirinta ta kasance abin a yaba. Wannan ne ya ba da damar yin hadin gwiwar da ta kai ga kashe mutum na biyu mafi girma a duniya a bangaren ta’addanci na ISIS.
Karfin soji ba zai magance matsalar tsaro ba

Kara karanta wannan
Kungiyar Izala ta yi magana kan bidiyon ɗan agaji da aka ji yana furta kalaman tashin hankali
Anderson ya ce karfin soji kadai ba zai iya magance matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta ba, ciki har da ta’addanci da satar mutane domin neman kudin fansa.
Ya kara da cewa zuba jari a shugabanci nagari da ci gaba na da muhimmanci wajen magance wadannan matsaloli.

Source: Twitter
Dangane da ficewar Mali, Burkina Faso da Nijar daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Anderson ya ce Amurka na kokarin sake bude tattaunawa da kasashen uku domin karfafa hadin gwiwar tsaro.
Ya kuma bayyana samar da kudaden tallafa wa ‘yan ta’adda, fashin teku, fasa-kwauri, safarar miyagun kwayoyi da kamun kifi ba bisa ka’ida ba a matsayin manyan matsalolin tsaro.
Anderson ya ce karuwar mayakan ISIS da ke mika wuya, tare da raguwar hare-hare da tashe-tashen hankula, na nuna ana samun ci gaba.
Ribadu ya gano matsalolin tsaro
Kun ji cewa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA), Nuhu Ribadu ya gano abubuwan da suka hana magance matsalar yan bindiga.
Nuhu Ribadu ya ce gibin bayanan sirri, raunin tsaron iyakoki, safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma ɗaukar matasa masu rauni aikin ta'addanci su ne manyan abubuwan da ke ƙarfafa ayyukan ’yan bindiga.
Asali: Legit.ng