Benjamin Netanyahu Ya Hango Faɗuwa, Ya Zargi Larabawa da Maguɗin Zaɓe

Benjamin Netanyahu Ya Hango Faɗuwa, Ya Zargi Larabawa da Maguɗin Zaɓe

  • Benjamin Netanyahu ya zargi jam'iyyun Larabawa da magudin zabe bayan sakamakon farko ya nuna cewa an bar shi a baya
  • Jam'iyyar Likud ta ce an samu cin hanci, barazana, tashin hankali da amfani da manhajojin da aka haramta, amma ba ta gabatar da hujjojin zargin a bainar jama'a ba
  • Netanyahu ya samu kujeru 53, yayin da jam'iyyun adawa suka samu 48, Larabawa 19; Shugaba Isaac Herzog zai fara tattaunawar kafa gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Isra'ila - Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi zargin an samu kura-kurai bayan kawancensa ya rasa rinjayen kujeru a Knesset.

Sai har zuwa yanzu ba ba a bayyana hujjoji ba kan zargin kuma har yanzu ba a kammala sakamakon zaben ba.

Netanyahu ya zargi tafka maguɗin zaɓe a Isra'ila
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Taylor Hill.
Source: Getty Images

Zargin Netanyahu kan zaben Isra'ila

Netanyahu ya zargi jam'iyyun siyasar Larabawa da magudin zabe bayan sakamakon farko ya nuna cewa kawancen siyasarsa bai samu rinjayen kujeru ba, cewar Anadolu.

Kara karanta wannan

Karya ta ƙare, masu bincike sun gano abin da ya yi sanadin mutuwar matasa 37 a ofishin NSCDC

Jam'iyyar ta ce tana da "daruruwan shaidu da hujjoji" da take shirin mika wa 'yan sanda, hukumar tsaro ta Shin Bet da kwamitin zabe na tsakiya.

Sai dai har yanzu ba a gabatar da wadannan hujjoji a bainar jama'a ba, babu kawancen siyasa da ya samu rinjayen kujeru a Knesset

Bayan an kirga mafi yawan kuri'un, kawancen Netanyahu ya samu kujeru 53 cikin 120 na majalisar dokoki.

Kawancen adawa karkashin jam'iyyar Yashar ta Gadi Eisenkot ya samu kujeru 48, yayin da jam'iyyun Larabawa Ra'am da United List suka samu 19.

Ana bukatar akalla kujeru 61 na majalisar dokoki domin kafa gwamnati mai rinjaye.

Netanyahu ya wallafa hoton fashewar makamin nukiliya a Tel Aviv da AI ta samar.

Rahotanni sun ce Netanyahu ka iya samun matsala a zaɓen Isra'ila
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Matakin da kwamitin zabe ya dauka a Isra'ila

A cewar The Times of Israel, kwamitin zabe yana nazarin korafin Likud. Sai dai wani babban jami'insa ya taba yin watsi da zarge-zargen magudin zabe a baya.

Kara karanta wannan

Taohon shugaban APC na Kano ya gamu da hatsari a hanyar dawowa daga wurin kamfen Tinubu

Shugaban adawa Gadi Eisenkot ya bayyana sakamakon a matsayin rashin nasarar Netanyahu, sannan ya bukace shi da ya yi murabus.

Shugaban Isra'ila Isaac Herzog zai fara tattaunawa da jam'iyyun siyasa mako mai zuwa domin kafa gwamnati.

Herzog ya jaddada cewa:

"Ya kamata mu yi duk mai yiwuwa domin kauce wa sake gudanar da wani zagayen zabe."

Sakamakon karshe na zaben na iya sauyawa, saboda har yanzu ba a kirga daruruwan dubban kuri'u ba, ciki har da na jami'an soji. Ana sa ran kammala kirga kuri'un zuwa karshen ranar Juma'a.

An yi zanga-zanga a Isra'ila

Mun ba ku labarin cewa dubban Isra’ilawa ne suka fito zanga-zanga a Tel Aviv domin nuna adawa da gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu a ranar Asabar.

Masu zanga-zangar sun bukaci kafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan harin Hamas na ranar 7 ga Oktoba, 2023, da abubuwan da suka gabace shi.

A cewar hukumomin Isra’ila, mayakan Hamas da wasu ƙungiyoyin Falasɗinawa sun kashe mutum kusan 1,200, tare da yin garkuwa da sama da 250.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.