Lauyan Pantami Ya Yi Magana kan Maido da Sunan Shi cikin 'Yan Takara

Lauyan Pantami Ya Yi Magana kan Maido da Sunan Shi cikin 'Yan Takara

  • Hukumar INEC ta dawo da sunan tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, cikin jerin ’yan takarar gwamnan Gombe na zaɓen 2027
  • Lauyan Pantami, Attahir Ibrahim, ya bayyana farin cikinsa da matakin, yana mai cewa yana da yakinin cewa ikon bayar da mulki na Allah
  • Lauyan ya ce ce-ce-ku-cen da ke tattare da takarar Pantami bai rage sha’awar jama’a a kansa ba, yana mai cewa mutane na goyon bayansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gombe – Lauyoyin Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami sun yi martani bayan Hukumar INEC ta dawo da sunan tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani cikin jerin ’yan takarar gwamnan jihar Gombe na zaɓen 2027.

Sai dai hukumar INEC ta bayyana cewa dawo da sunan Pantami na ƙarƙashin sakamakon shari’o’in da ke gaban kotu.

Kara karanta wannan

"Yadda cire sunan Aminu Gwarzo da INEC ta yi ya zama alheri ga NDC a jihar Kano"

Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami a wajen taron PDP. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Lauyan Isa Pantami ya yi magana

Jaridar Leadership ta rahoto cewa wani mamba a tawagar lauyoyin Pantami, Attahir Ibrahim, ya bayyana cewa bai damu da ce-ce-kucen da ke tattare da takarar ba, yana mai cewa dawo da sunan tsohon ministan abin farin ciki ne.

Attahir ya ce a wata hira da aka yi da shi:

“Ko da yake ban taɓa damuwa da lamarin ba, abu ne da ya kamata a yi farin ciki da shi.”

Lauyan ya danganta kwarin gwiwarsa da imanin cewa ikon mulki na Allah ne, yana mai cewa fafatawar siyasa da ƙoƙarin hana wasu mutane samun mukaman shugabanci ba sabon abu ba ne a tarihi.

Ya ƙara da cewa:

“Duk wanda ya fahimci tarihin mulki da fafatawar siyasa a duniya, ba zai yi mamaki ko tsoro da duk abin da ya faru ba. Wannan kuwa saboda na san cewa iko na Allah ne. Idan Ya yanke shawarar ba wa mutum mulki, ko da me wani zai yi, ba zai iya hana hakan ba.”

Kara karanta wannan

Abba Hikima ya fito da abin da ya kamata mutane su sani kan takarar Pantami da Aminu Gwarzo

Lauyoyin Sheikh Pantami na sa ran nasara

Barista Attahir ya kuma yi magana kan abin da ya bayyana a matsayin maimaita shari’o’i da sauye-sauyen matsaya daga ɓangarorin da ke cikin takaddamar.

Ya ce tawagarsu na da kyakkyawan fata cewa tsarin shari’a zai haifar da sakamakon da zai ba Pantami nasara.

Lauyan ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa tsawon lokacin da aka shafe ana takaddama kan takarar na iya rage magoya bayan tsohon ministan.

Sheikh Pantami a ofis
Dan takarar PDP, Sheikh Isa Ali Pantami. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda ke tuntuɓarsa ’yan uwa ne, abokai da magoya baya waɗanda ba su taɓa sanin Pantami kai tsaye ba.

Bugu da kari, Attahir ya ƙara da cewa wani gidan rediyo ma ya tuntuɓe shi domin yin hira da shi kan batun takarar da dawo da sunan Malam.

An yi murnar dawowar Pantami

A wani labarin, kun ji cewa al’ummar jihar Gombe sun fito kan tituna cikin dare domin murnar dawo da sunan Farfesa Isa Ali Pantami cikin jerin ’yan takarar gwamnan jihar na zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

An barke da murna a Gombe da INEC ta dawo da Pantami cikin takara

Masu goyon bayan Pantami sun yi jerin gwanon motoci da babura a unguwannin Pantami, Jekadafari, Bolari da Tudun Wada da sauransu.

Wani mai goyon bayan ADC ya bayyana farin cikinsa da matakin, yana mai cewa hakan na iya rage ƙuri’un APC da PDP a jihar Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng