An Jero Sunayen Malaman da aka Sace za Su Tafi yi wa Tinubu Addu'ar Nasara

An Jero Sunayen Malaman da aka Sace za Su Tafi yi wa Tinubu Addu'ar Nasara

  • An kwashe sa’o’i 48 tun bayan sace malaman addinin Musulunci 6 a karamar hukumar Bakura ta jihar Zamfara, amma ’yan bindigar ba su tuntubi iyalansu ba
  • Mafi yawancin malaman da aka sace manyan limaman Juma’a ne, ciki har da limamin babban masallacin Juma’a na Dakko da mataimakinsa
  • Mazauna yankin sun bayyana fargabar cewa rashin samun labarin malaman ya jefa iyalansu da al’ummominsu cikin dimuwa, yayin da ake neman inda suke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – ’Yan bindiga sun yi awon gaba da malaman addinin Musulunci 6, mafi yawansu manyan limaman masallatan Juma’a, a karamar hukumar Bakura ta jihar Zamfara.

Sa’o’i 48 bayan sace malaman, har yanzu ’yan bindigar ba su tuntubi iyalansu domin neman kudin fansa ba.

Kara karanta wannan

Wasu malaman musulunci sun faɗa tarkon yan bindiga a hanyar dawowa daga taron APC

Malaman Musulunci da aka sace
Malaman da aka ce sun je taron APC a Zamfara. Hoto: @Danbakatsina50
Source: Twitter

Yadda aka sace malaman 6

Daily Trust ta ruwaito cewa mazauna kauyen Dakko sun ce limamin masallacin Juma’a na yankin, Malam Muhammadu Shehu, da mataimakinsa, Malam Murtala Dakko, na cikin malaman da aka sace.

Wani mazaunin yankin, Malam Musa Dakko, ya ce al’ummar yankin na cikin wani hali na fargaba saboda ba su san ko malaman suna raye ko an kashe su ba.

Ya ce:

“Mun yi tsammanin ’yan bindigar za su tuntubi iyalan malaman da wuri, ganin irin matsayin da suke da shi a cikin al’umma, amma har yanzu ba su yi hakan ba.
“Muna cikin matukar tashin hankali saboda ba mu san ko malaman suna raye ko an kashe su ba. Wannan rashin tabbas kadai ya isa ya jefa al’umma cikin damuwa. Muna son a dawo mana da malamanmu.”

Ga sunayen malaman da aka sace

Malaman da aka yi awon gaba da su sun hada da:

Kara karanta wannan

Gargadin ƴan sanda ga al'ummar Sokoto bayan hari kan Sheikh Lukuwa a masallaci

  • Malam Muhammadu Shehu, babban limamin masallacin Juma’a na Dakko.
  • Malam Murtala Dakko, mataimakin limamin masallacin Juma’a na Dakko.
  • Malam Muhammad Yahuza, babban limamin masallacin Juma’a na Dogon Madacci na 1.
  • Malam Magawata Abdullahi, babban limamin masallacin Juma’a na Dogon Madacci na 2.
  • Malam Bala Hogun, babban limamin masallacin Juma’a na Hogun.
  • Malam Muhammad Tasi’u, babban limamin masallacin Juma’a na Kwatsama.

Bayanan da aka tattara tattara sun nuna cewa ’yan bindigar sun sace malaman ne ranar Asabar a kauyen Gidan Bature da ke unguwar Damri, karamar hukumar Bakura.

Malaman 5 daga cikinsu ’yan asalin Bakura ne, yayin da daya ya fito daga karamar hukumar Anka.

Taswirar jihar Zamfara
Taswirar jihar Zamfara a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Dabarar sace malaman

Wani rahoto daga wasu majiyoyi da dama sun tabbatar da sace malaman, inda suka ce ’yan bindigar sun yi musu kwanton bauna tare da tafiya da su.

Majiyar ta ce ana zargin masu satar mutanen sun san hanyar da malaman za su bi tun kafin su fara tafiya.

Malamai sun goyi bayan Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce malaman mata na Arewa sun amince da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Uba Sani ya ce malaman ba su goyi bayan Tinubu saboda son zuciya ko wata manufa ta kashin kai ba, sai dai saboda abin da ya ce shugaban ya yi wa Arewa.

Rahoto ua nuna cewa gwamnan ya ce sun yabawa Tinubu kan nasarorin da ya samu a bangarorin ilimi, ayyukan more rayuwa, kiwon lafiya da noma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng