An Bude wa Tawagar Dan Takarar Gwamnan ADC Wuta da Bindiga a Sokoto
- Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun bude wa ayarin motocin dan takarar gwamnan jam’iyyar ADC a Sokoto, Mannir Muhammad Dan’iya, wuta a kusa da filin jirgin saman jihar
- Dan’iya ya tsira ba tare da rauni ba, amma rahotanni sun ce harbin ya lalata wasu daga cikin motocin masu sulke da ke cikin ayarin nasa
- Yayain da ake cigaba da jiran karin bayani daga jami'an tsaro, dan takarar ya zargi jami’an tsaro da hana shi wucewa tare da tsare jami’an DSS biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Dan takarar gwamnan jihar Sokoto a jam’iyyar ADC, Hon. Mannir Muhammad Dan’iya, ya tsira daga harin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai wa ayarin motocinsa a daren Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na dare, kusa da filin jirgin saman Sultan Abubakar III, jim kadan bayan Dan’iya ya raka tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, zuwa filin jirgin.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Vanguard ya ce harin ya yi sanadin lalacewar wasu daga cikin motocin masu sulke da ke cikin ayarin dan takarar.
Bayanin 'yan sandan Sokoto
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufae, ya tabbatar da cewa rundunar ta samu rahoton abin da ya faru a yankin filin jirgin saman.
Ya ce rundunar za ta dauki matakan da suka dace, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu a lamarin zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan wadanda suka bude wuta ko musabbabin harin ba.
Maganar dan takarar ADC
A wata sanarwa da hadiminsa kan harkokin yada labarai, Aminu Abdullahi, ya fitar, Dan’iya ya yi zargin cewa jami’an rundunar Sokoto Marshal da Community Guard sun tare ayarin motocinsa tare da hana shi wucewa ta yankin filin jirgin.
Leadership ta rahoto cewa sanarwar ta ce jami’an sun yi ikirarin cewa suna aiki ne bisa umarnin shugabanninsu na hana mambobin ADC shiga jihar Sokoto.
Ta kara da cewa jami’an tsaron dan takarar sun yi kokarin shawo kan lamarin, amma hakan bai yiwu ba kafin daga bisani aka bude wuta, lamarin da ya lalata motocin masu sulke.
Dan’iya ya kuma yi zargin cewa an tsare jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) guda biyu da aka sanya wa ayarinsa domin kare shi.
Dan takarar ya bukaci bincike
Dan’iya ya bayyana lamarin a matsayin barazana ga tsaron rayuwarsa da kuma ’yancin siyasa da dimokuradiyya a jihar.
Ya ce tun a ranar Juma’a tawagarsa ta lura da yadda jami’an Sokoto Marshal da Community Guard suka bazama a wasu hanyoyin shiga jihar, inda ake zargin sun hana motocin da ke dauke da tambarin ADC shiga.
Ya bayyana cewa abin da farko ya yi kama da aikin tsaro na yau da kullum ya fara tayar da hankalin tawagarsa kan yiwuwar kokarin takaita zirga-zirga da ayyukan siyasa na ’yan adawa.
Dan’iya ya ce ya kai rahoton lamarin ga kwamishinan ’yan sandan jihar domin bayyana abin da ya faru da kuma neman daukar mataki.
Ya bukaci Sufeto Janar na ’yan sanda, Darakta Janar na DSS da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da bincike, gano wadanda ke da hannu tare da tabbatar da ko an bayar da umarnin da ya saba wa doka.

Source: Original
Ya kuma bukaci a saki jami’an DSS din biyu idan har suna tsare, tare da adana bidiyon da aka dauka, bayanan ayyukan jami’an tsaro da shaidun wadanda suka ga abin da ya faru domin gudanar da bincike na gaskiya.
Sai dai zarge-zargen da ke cikin sanarwar ADC ba su samu tabbaci mai zaman kansa ba a lokacin hada wannan rahoto..
An kai wa Sowore hari
A wani labarin, kun ji cewa wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne sun kai hari kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore a Ado-Ekiti, jihar Ekiti.
Sowore ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, inda ya ce wasu bata-gari sun farmake shi da tawagarsa a cikin gidan abincin.
Dan takarar shugaban kasar ya rubuta cewa “wasu bata-gari sun kawo mana hari a cikin wani gidan cin abinci a Ado-Ekiti” yayin da ya ke neman agaji.
Asali: Legit.ng


