Obasanjo Ya Tona Yadda Gwamnatin Tinubu Ta Jefa 'Yan Najeriya cikin Talauci

Obasanjo Ya Tona Yadda Gwamnatin Tinubu Ta Jefa 'Yan Najeriya cikin Talauci

  • Obasanjo ya zargi sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu da ƙara jefa ’yan Najeriya cikin talauci, musamman sakamakon faduwar darajar Naira
  • Ya ce darajar Naira ta faɗi daga kusan N500 zuwa dala ɗaya zuwa N1,500, yana mai cewa hakan ya rage ƙarfin sayen ’yan Najeriya
  • Gwamnatin Tinubu ta cire tallafin man fetur tare da sauya tsarin kasuwar canjin kuɗaɗe, matakan da suka zo da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Landan - Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya soki manufofin da gwamnatin Bola Tinubu ta aiwatar.

Obasanjo ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar, ciki har da rage darajar Naira, sun ƙara tsananta talauci a ƙasar.

Obasanjo ya soki gwamnatin Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na gaisawa tare da Olusegun Obasanjo Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Obasanjo ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 21, ga watan Oktoban 2026 yayin taron Financial Times Africa Summit 2026, wanda aka gudanar a Landan, babban birnin Birtaniya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tinubu ya jingine bambancin siyasa, ya aika da muhimmin sako ga Kwankwaso

A cewarsa, faduwar darajar Naira cikin sauri ta jefa ’yan Najeriya cikin matsin tattalin arziki, tare da taimakawa wajen sanya ƙasar cikin jerin ƙasashen da ke da mafi yawan talakawa a duniya.

Obasanjo ya soki faduwar darajar Naira

Tsohon shugaban ƙasar ya ce ba za a iya ware tattalin arzikin Najeriya daga sauran ƙasashen duniya ba, don haka sauye-sauyen da ake yi wa darajar kuɗin ƙasar suna da tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a.

“Ba ma rayuwa a keɓe a matsayin ƙasa. Muna hulɗa da sauran ƙasashen duniya. Amma cikin dare ɗaya, sai ka rage darajar kuɗinka da kashi 300 cikin 100. Naira ta tashi daga N500 kan dala ɗaya zuwa N1,500 kan dala ɗaya.
“Abin da hakan ke nufi shi ne, kowane ɗan Najeriya ya talauce da kashi 300 cikin 100. Wannan ya sa Najeriya ta zama ƙasar da ke da mafi yawan talakawa a duniya, wato ƙasar da ke da adadi mafi girma na talakawa.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya hango matsala a dokar zabe da za ta iya shafar sahihancin zaben 2027

“Ba za ka ce mini wannan abu ne mai kyau ga Najeriya ba. Ba za ka ce mini yana da amfani gare mu ta kowace fuska ba.” In ji shi.

An cire tallafin fetur da yin sauyi a kasuwar kudi

A watan Mayun 2023, Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, matakin da ya janyo tashin farashin man fetur da kuɗin sufuri a sassa daban-daban na ƙasar.

A watan Yunin 2023 kuma, gwamnatinsa ta fara sauye-sauyen kasuwar canjin kuɗaɗe, inda ta bai wa Naira damar yin ciniki bisa yanayin kasuwa cikin ’yanci fiye da baya, tare da rushe tsarin musayar kuɗaɗe da ke da farashi daban-daban.

Gwamnati ta bayyana cewa an yi waɗannan sauye-sauye ne domin inganta kasuwar canjin kuɗaɗe, jawo masu zuba jari 'yan ƙasashen waje da kuma gyara matsalolin da suka daɗe suna addabar kasuwar.

Sai dai matakan sun zo ne a daidai lokacin da darajar Naira ta faɗi sosai, hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru, sannan kayan da ake shigowa da su daga ƙasashen waje suka ƙara tsada.

Obasanjo ya soki Tinubu
Olusegun Obasanjo na jawabi a wajen taro Hoto: Alex C. Otti
Source: Facebook

Atiku ya ce ya ceci Obasanjo

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya fadi dalilin da ya sa tawagar kamfen din Tinubu ke ziyartar sarakuna

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya bayyana yadda ya ce ya ceci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo daga wata allura da ake zargin an shirya yi masa a gidan yari.

Atiku ya ce ya fallasa bayanan shirin yin allurar tare da gargadin Obasanjo kada ya amince a yi masa ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng