2027: Ana Zargin Wasu Kusoshin APC Sun Fito da Kudi don Ruguza Shirin Hadewar Yan Adawa

2027: Ana Zargin Wasu Kusoshin APC Sun Fito da Kudi don Ruguza Shirin Hadewar Yan Adawa

  • Jam’iyyar PRP ta zargi wasu mambobin jam’iyya mai mulki da shirin haddasa rikici domin ruguza ƙoƙarin haɗa kan ’yan adawa gabanin zaɓen 2027
  • Jam’iyyar ta yi gargaɗi kan ɗaukar wakilan rumfunan zaɓe da sunanta ba tare da izini ba, tana zargin cewa ana iya amfani da kuɗi wajen rinjayar mambobinta
  • Shugaban PRP na ƙasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce jami’an jam’iyyar da ake zargi da hannu a shirin za su fuskanci matakin ladabtarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar PRP ta zargi wasu mambobin jam’iyya mai mulki, APC da ƙulla makircin da zai haddasa rabuwar kai tsakanin yan adawa gabanin zaben 2027.

Jam’iyyar ta kuma yi gargaɗi kan yunƙurin ɗaukar wakilan rumfunan zaɓe da sunanta daga wasu mutane da ta ce ba su da izinin yin hakan.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano masu shirya kai farmaki kan matasan da za su y aikin zaɓen 2027

Hakeem.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Hakeem Baba Hamed Hoto: Hakeem Baba Ahmed
Source: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar da sanyin safiyar Alhamis, 22 ga Oktoba, wadda shugaban PRP na ƙasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya sanya wa hannu.

PRP ta zargi wasu 'yan APC da shirin raba kai

PRP ta yi zargin cewa ana amfani da wasu tsofaffin mambobinta da jami’an da ke aiki a yanzu wajen haifar da rarrabuwar kai da raunana goyon bayan da take da shi a matakin ƙasa.

Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa manyan mambobin jam’iyya mai mulki ne suka ɗauki nauyin wannan shiri da ɗaruruwan miliyoyin Naira.

PRP ta buƙaci mambobinta da sauran jama’a su yi watsi da yunƙurin ɗaukar wakilan rumfunan zaɓe ba tare da izini ba, tana zargin cewa ana iya amfani da kuɗi wajen rinjayar mambobinta su goyi bayan ’yan takarar ’yan adawa.

Jam’iyyar ta kuma gargaɗi jami’anta da ake zargin suna da hannu a shirin cewa za su fuskanci matakin ladabtarwa.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Makinde ya fallasa shirin gwamnatin APC kan jam'iyyun adawa

“PRP tana sanar da mambobinta da sauran jama’a game da waɗannan yunƙuri, tare da gargaɗin kada su faɗa tarkon goyon bayan waɗannan mutane masu yunƙurin lalata ta,” in ji sanarwar.

PRP ta buƙaci mutanen da ke cikin jam’iyya mai mulki da ake zargin suna da hannu a makircin da su nisanta kansu daga abin da ta bayyana a matsayin ƙoƙarin ƙirƙirar wata jam’iyyar PRP ta bogi ta hanyar amfani da kuɗaɗensu da sunayensu.

Jam'iyyar PRP ta karfafa guiwar mambobinta

Baba-Ahmed ya tabbatar wa ’yan takarar jam’iyyar da magoya bayanta cewa shugabancinta ba zai yi watsi da alƙawuran da ya ɗauka da amincin da suka nuna mata ba.

APC Nig.
Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: @nentawe1
Source: Twitter

Ya ce jam’iyyar na nan daram kan matsayarta na ƙalubalantar ci gaba da mulkin gwamnatin da ke kan karagar mulki bayan shekarar 2027, tare da ba da gudummawa wajen kafa haɗakar ’yan adawa da za ta iya samun nasara a zaɓe.

PRP ta ce Bola Tinubu ya gaza

Kun ji cewa shugaban PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙara ta’azzara matsin tattalin arziki da rashin tsaro a Najeriya.

Ya bayyana bangarorin tattalin arziki da tsaro a matsayin wadanda Tinubu ya yi mummunan gazawa, wanda har yanzu yan Najeiya ba su amfana da tsare-tsaren da ya kawo ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262