Tinubu Ya Tsauyawa Matasan da Aka Kama kan Jifan Motocinsa a Masallacin Juma'a

Tinubu Ya Tsauyawa Matasan da Aka Kama kan Jifan Motocinsa a Masallacin Juma'a

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin sakin mutanen 78 da aka kama bisa zargin hannu a harin da aka kai wa ayarinsa a ranar Juma’a
  • Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya ta ce an umarci a yi wa waɗanda ake zargin gargadi sannan a sake su bayan shugaban ƙasa ya yi musu afuwa
  • An kai harin ne bayan Tinubu ya idar da sallar Juma’a a wani masallaci da ke unguwar Garki a Abuja, inda wasu matasa suka jefi ayarinsa da duwatsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin sakin mutanen da aka kama bisa zargin hannu a harin da aka kai wa ayarinsa a ranar Juma’a.

An ruwaito cewa wasu matasa da suka fusata sun jefi ayarin motocin shugaban ƙasar da duwatsu bayan ya fito daga wani masallaci da ke unguwar Garki a Abuja, tare da ihum ba ma yi.

Kara karanta wannan

"Yadda Pater Obi da Kwankwaso za su kifar da Tinubu a zaben 2027 da taimakon Allah"

Jaridar Daily Truat ta ruwaito cewa bayan faruwar lamarin, rundunar ’yan sandan Abuja ta kama mutum 78 da ake zargi da hannu a lamarin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, Josephine Adeh, kakakin rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya (FCT), ta ce an yi wa waɗanda ake zargin afuwa.

“Rundunar ’yan sandan Abuja na sanar da jama’a cewa ta kama mutum 78 bayan harin da aka kai wa ayarin motocin shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunonin sojojin ƙasar nan, Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2026, a wani masallaci da ke unguwar Garki, Abuja.

“Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan shugaban ƙasa ya idar da sallar Juma’a lokacin da wasu mutane suka kai wa ayarin motocin da ke tafiya hari da duwatsu da wasu abubuwa masu haɗari.

"Harin ya lalata motoci da dama tare da jikkata wasu jami’an tsaro. Wata tawagar jami’an tsaro ta haɗin gwiwa, ƙarƙashin jagorancin ’yan sanda, ta gaggauta kai dauki tare da kama mutane 78.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta yi martani kan rahoton kai wa tawagar Tinubu hari

Sai dai rundunae yan sandan ta tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya yi wa matasan afuwa, kuma ya bada umarnin a sake su.

“Shugaban ƙasa ya yi wa mutanen da ke da hannu a harin afuwa, sannan fadarsa ta ba da umarnin gargadin waɗanda aka kama kuma a sake su.

"Bisa bin wannan umarni, rundunar na sanar da jama’a cewa a halin yanzu ana kammala matakan da suka dace domin sakin waɗanda ake zargin.

Kwamishinan ’yan sandan babban birnin tarayya, CP Ahmed Mohammed Sanusi, PhD, FCAI, ya yi gargaɗi kan aikata laifukan tashin hankali, tayar da tarzoma da lalata dukiyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262