An Faɗi Gwamnatin da Ministoci ke Biyan Biliyoyi domin Samun Muƙami

An Faɗi Gwamnatin da Ministoci ke Biyan Biliyoyi domin Samun Muƙami

  • Felix Morka, kakakin APC na ƙasa, ya musanta zargin cewa ministocin gwamnatin Bola Tinubu sun biya biliyoyin naira domin samun muƙamansu
  • Morka ya ce Alwan Hassan yana magana ne kan gwamnatocin baya, ba gwamnatin Tinubu ba, lokacin da ya yi zargin cewa ministoci suna biyan kuɗi domin samun muƙamai
  • Kakakin APC ya jaddada cewa ana naɗa ministocin gwamnatin Tinubu bisa cancanta, ƙwarewa da ikon gudanar da ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Felix Morka, sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC na ƙasa, ya yi magana kan zargin biyan kudi domin ba ministoci muƙami.

Morka ya yi watsi da zargin cewa ministocin da ke aiki a ƙarƙashin Bola Tinubu sun biya biliyoyin naira domin samun muƙamansu.

APC ta musanta cewa ministoci na biyan na goro saboda mukami
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Morka ya ƙaryata zargin ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV ranar Laraba.

Kara karanta wannan

To fa: ADC ta fallasa makarkashiyar da ake shiryawa kan zaben 2027, ta ja kunnen Tinubu

Zargin ba da na goro kan muƙaman ministoci

Alwan Hassan, mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, ya yi zargin cewa wasu ministoci sun biya biliyoyin naira domin samun naɗinsu, kuma sun shiga ofis da niyyar kwato kuɗaɗen da suka kashe.

Hassan ya yi zargin cewa wasu ministoci suna biyan makudan kuɗaɗe domin samun naɗin muƙamai.

Ya kuma yi iƙirarin cewa wannan al’ada ba ta takaita ga APC ba, yana mai cewa ministoci sun kasance cikin jami’an gwamnati mafi yawan aikata rashawa a gwamnatoci daban-daban.

Hassan ya ce:

“Charles, ministoci da yawa suna biyan biliyoyi da biliyoyi domin a naɗa su. Abu na farko da suke tunani shi ne yadda za su dawo da kuɗin da suka kashe.”

Martanin APC kan zarge-zargen

Morka ya ce kalaman Hassan da suka jawo ce-ce-ku-ce suna magana ne kan gwamnatocin baya, ba gwamnatin da ake ciki yanzu ba.

Kara karanta wannan

"Bai cancanta ba," An tono abin da zai iya zama matsala ga abokin takarar Atiku a 2027

Morka ya ce:

“Idan ana magana a bainar jama’a, mutane suna da hanyoyi daban-daban na bayyana ra’ayoyinsu. Tun bayan hirar, na samu damar tattaunawa da Alwan domin fahimtar abin da yake nufi lokacin da ya yi waɗannan kalamai.
“Ya bayyana mini cewa ba wannan gwamnatin yake magana a kanta ba, sai dai yana magana ne kan abubuwan da suka faru a tarihi."

A gaskiya, yana nufin cewa ministoci a ƙasarmu sun daɗe suna da mummunan tarihin shiga irin wannan hali.”

Morka ya ce ana naɗa ministoci a gwamnatin Tinubu ne bisa cancanta, ƙwarewa da ikon gudanar da ayyuka, ba wai saboda sun biya kuɗaɗe domin samun muƙamai ba.

Uzodinma: APC ta yi fatalo da hukuncin kotu

A wani labarin, an ji cewa APC a jihar Imo ta ce Gwamna Hope Uzodimma ne har yanzu ɗan takararta na kujerar sanatan Imo ta Yamma.

A zaɓen 2027, jam’iyya mai mulki ta nuna ba ta san da batun takarar Rochas Okorocha ba, ba shi ne ya ci zabe ba.

Duk da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta amince da nasarar Rochas Okorocha, ba a so a sauya Uzodinma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.