Jigo a APC Ya Tona Asirin Ministocin Gwamnatin Tinubu

Jigo a APC Ya Tona Asirin Ministocin Gwamnatin Tinubu

  • Alwan Hassan ya yi zargin cewa wasu ministoci na biyan biliyoyin naira domin samun muƙamai a gwamnati
  • Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ya bayyana cewa matsalar ta wanzu tun kafin jam’iyyar ta hau mulki, tare da tambayar muhimmancin ba ministoci kasafin kuɗi
  • Alwan Hassan ya yi hasashen cewa ayyukan da Shugaba Bola Tinubu ya gudanar a wasu yankunan Arewa za su taimaka masa wajen samun ƙuri’u a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Alwan Hassan, mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya yi zargi kan ministoci.

Alwan Hassan ya yi zargin cewa wasu ministoci na biyan biliyoyin naira domin samun muƙamai a gwamnati, sannan su mayar da hankali wajen dawo da kuɗin da suka kashe.

Alwan Hassan ya yi zargi kan ministoci
Jigo a jam'iyyar APC, Alwan Hassan Hoto: Alwan Hassan
Source: Facebook

Alwan Hassan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise News ta yi da shi ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan

2027: Ana zargin wasu ƙusoshin APC sun fito da kudi don ruguza shirin hadewar yan adawa

Jigon na APC ya zargi ministoci da kasancewa cikin jami’an gwamnati da suka fi aikata cin hanci da rashawa.

Ya ce wannan dabi’a ba ta fara ne a ƙarƙashin gwamnatin APC ba, domin a cewarsa, ta samo asali tun kafin jam’iyyar ta karɓi mulki.

Ya ce ministoci na kokarin mayar da kudadensu

Alwan Hassan ya bayyana cewa ministoci na daga cikin jami’an da ake yawan zargi da aikata manyan laifuffukan almundahana bayan kammala wa’adin kowace gwamnati.

“Duk lokacin da gwamnati ta bar mulki, ministoci ne suka fi kasancewa cikin waɗanda suka aikata manyan laifuffuka a cikin gwamnati,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa wasu ministocin kan kashe makudan kuɗaɗe domin samun muƙamai, abin da a cewarsa ke sa su fara tunanin yadda za su dawo da kuɗin bayan an naɗa su.

“Ministoci da dama na biyan biliyoyin naira domin a naɗa su, kuma abu na farko da suke tunani bayan sun samu muƙamin shi ne yadda za su dawo da kuɗin da suka kashe,” in ji Alwan Hassan.

Kara karanta wannan

Limamin masallaci ya tsoma kansa a matsala kan tallata Shugaba Tinubu

Ya jaddada cewa wannan shi ne abin da yake ganin yana faruwa a ƙasar, yana mai cewa ba ministocin APC kaɗai abin ya shafa ba, domin matsalar ta wanzu tun kafin jam’iyyar ta hau mulki.

Alwan Hassan ya kuma yi zargin cewa ministoci na daga cikin mutanen da hukumomi ke kamawa kan zargin almundahana bayan kowace gwamnati ta kammala wa’adinta.

Ya soki rawar da ministoci ke taka wa

A yayin hirar, Alwan Hassan ya kuma nuna shakku kan yadda ake bai wa ministoci alhakin gudanar da kasafin kuɗi, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali kan samar da kuɗin aiwatar da kasafin da aka amince da shi.

“Me ya sa muke buƙatar ministoci? Me ya sa ake buƙatar bai wa ministoci kasafin kuɗi?” ya tambaya.

Jigon APC ya yi maganar Tinubu

Da yake magana kan babban zaɓen 2027, Hassan ya bayyana kwarin gwiwar cewa ayyukan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gudanar a wasu sassan Arewa za su taimaka masa wajen samun ƙuri’u.

Ya yi iƙirarin cewa ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Tinubu ta gudanar a wasu yankunan Arewa za su iya sauya ra’ayin masu zaɓe a jihohin da shugaban ya sha kaye a zaɓen 2023, ciki har da Kano da Bauchi.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Makinde ya fallasa shirin gwamnatin APC kan jam'iyyun adawa

“A shekarar 2023, Asiwaju ɗan takara ne, ba shugaban ƙasa ba. Ya gudanar da ayyuka da dama a wurare kamar Kano, sannan ya gyara tituna da dama a Arewa, waɗanda za su iya jawo masa ƙuri’u,” in ji shi.
Alwan Hassan ya yi magana kan ministoci
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

An hango faduwar Tinubu a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa Dele Momodu, ya bayyana cewa babu wata dabarar siyasa da za ta ceci Shugaba Bola Tinubu daga shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Jigon na ADC ya bayyana cewa yunwa da matsin rayuwa da ’yan Najeriya ke fuskanta za su yi tasiri sosai wajen tantance sakamakon zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng