Rigima Sabuwa: ADC Ta Fallasa Makarkashiyar da Ake Shiryawa kan Zaben 2027
- Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC ya yi zargin cewa ana wani shiri kan zaben 2027
- ADC ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi watsi da duk wani yunƙuri na sauya ranar zaɓe, tare da yin kira ga shugaban INEC
- Jam’iyyar ta ce bai kamata a yi amfani da barkewar cutar Ebola a matsayin hujjar jinkirta zaɓe ba, tana mai cewa NCDC ta bayyana cewa babu dalilin yin hakan a halin yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya yi zargi kan zaben shekarar 2027.
Kwamitin na ADC ya yi zargin cewa ana shirin matsa wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) lamba domin sauya ranar zaɓen shugaban ƙasa da aka tsara gudanarwa ranar 16 ga Janairun 2027.

Kara karanta wannan
Farfesa ya kunyata NDC ta su Kwankwaso da Obi bayan ganin sunansa a kwamitin kamfe

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa dabarun sadarwa na kwamitin, Phrank Shaibu, ya fitar a shafinsa na X ranar Laraba, 28 ga watan Oktoban 2026.
Kwamitin ya gargaɗi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya yi yunƙurin kauce wa hukuncin da ’yan Najeriya za su yanke ta hanyar jefa ƙuri’a.
A cewar kwamitin, ya samu bayanan sirri cewa za a gayyaci shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, zuwa fadar shugaban ƙasa, inda za a umurce shi da ya sauya jadawalin zaɓen, duk da cewa kwanaki 80 ne kawai suka rage kafin zaɓen.
ADC ta mika bukatarta ga INEC
A cikin sanarwar ADC ta buƙaci Tinubu da ya yi watsi da duk wani yunƙuri na sauya ranar zaɓen.
Haka kuma, ta buƙaci Amupitan da ya ƙi bin duk wani umarni da za a ba shi na sauya ranar zaɓen, tare da bayyana wa jama’a nan take idan aka yi masa irin wannan matsin lamba.
Kwamitin ya ce ranar zaɓe mallakin ’yan Najeriya ce, don haka bai kamata a sauya ta a ɓoye ba tare da sanar da jama’a ba.
Ya ƙara da cewa ’yan Najeriya sun shafe shekaru uku da rabi suna fuskantar tashin farashin kayayyaki, raguwar kuɗaɗen shiga da kuma matsin tattalin arziki.
Saboda haka, ya ce ya kamata a ba su damar bayyana ra’ayinsu kan yadda gwamnatin Tinubu ta gudanar da mulki ta hanyar jefa ƙuri’a a ranar 16 ga Janairu.
ADC ta yi gargadi kan amfani da Ebola
Kwamitin ya bayyana cewa bai kamata gwamnati ta yi amfani da matsalar lafiya wajen neman jinkirta zaɓe ba, duk da cewa ya amince cewa cutar Ebola babbar barazana ce ga lafiyar jama’a.
Ya ce ya kamata a bar ƙwararrun ma’aikatan lafiya su ɗauki matakan da suka dace domin shawo kan cutar, yayin da INEC za ta tabbatar da kare lafiyar masu zaɓe da ma’aikatan zaɓe.
ADC ta kuma yi nuni da matsayin babban daraktan Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), wanda a cewarta, ya bayyana cewa babu wani dalili a halin yanzu da zai sa a dage zaɓen.
Kwamitin ya gargaɗi gwamnati da kada ta mayar da matsalar Ebola wata hujjar siyasa domin jinkirta zaɓe.
An buƙaci bayyana duk wani shiri a fili
ADC ta kuma ja hankalin INEC, masu sa ido kan zaɓe na cikin gida da kuma masu sa ido na ƙasashen waje kan batun.
Ta buƙaci duk wani shiri na sauya jadawalin zaɓe ya fito fili, tare da gabatar da hujjojin lafiya da aka wallafa domin jama’a su tantance su.
A cewar kwamitin, bai kamata fadar shugaban ƙasa ta yi amfani da matsalar lafiya wajen guje wa hukuncin da ’yan Najeriya za su yanke ta hanyar zaɓe ba.

Source: Facebook
ADC za ta yi wa INEC kishiya
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar ADC mai adawa ta ce ita da kan ta za ta tattara kuri’un da aka kada mata a lokacin zaben shekarar 2027.
Babbar jam’iyyar hamayyar ta ce tattarawa da wallafa sakamakon zaben da za ta yi yana cikin damar da ta ke da ita.
Asali: Legit.ng
