Abubuwa 10 da Ya Kamata Ma'aikata Su Sani kan Tallafin N70,000 duk Wata

Abubuwa 10 da Ya Kamata Ma'aikata Su Sani kan Tallafin N70,000 duk Wata

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan ma’aikatan gwamnati alawus ɗin sufuri na N70,000 duk wata na tsawon watanni shida, domin rage tasirin tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

An cimma wannan matsaya ne a taron sasanta rikici tsakanin gwamnatin tarayya da Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), wanda aka gudanar a Abuja ranar 27 ga Oktoba, 2026.

NLC ta cimma yarjejeniya da gwamnati
Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, na jawabi a wajen taron kungiyar Hoto: @NLCHeadquarters
Source: Twitter

Yarjejeniyar ta ƙunshi batutuwan jin daɗin ma’aikata, biyan basussukan alawus-alawus, hakkokin ma’aikatan lafiya da tattaunawar mafi ƙarancin albashi, cewar rahoton jaridar The Punch.

Ga muhimman abubuwa 10 da ya kamata a sani game da yarjejeniyar.

1. Za a biya N70,000 duk wata

Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan N70,000 a kowane wata a matsayin tallafin sufuri ga ma’aikatan gwamnati.

Takardar yarjejeniyar ta nuna cewa tallafin zai shafi ma’aikata a dukkan matakai. yarjejeniyar ta nuna cewa tallafin zai shafi ma’aikata a dukkan matakai.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: TUC ta kawo cikas a shirin gwamnatin Tinubu na fara rabon tallafin N70,000

2. Za a fara biyan kuɗin a Nuwamba 2026

An tsara fara biyan alawus ɗin a watan Nuwamba na shekarar 2026.

Sai dai takardar ba ta bayyana takamaiman ranar da za a fara biyan kuɗin ba, ko kuma ko za a riƙa haɗa shi da albashin wata-wata.

3. Shirin zai ɗauki watanni shida

Tallafin na ɗan lokaci ne, kuma zai ɗauki watanni shida daga Nuwamba 2026 zuwa Afrilu 2027, bisa aiwatar da yarjejeniyar.

4. Kowane ma’aikaci zai iya samun jimillar N420,000

Idan aka biya ma’aikaci N70,000 a kowane wata na tsawon watanni shida, jimillar kuɗin da zai samu za ta kai N420,000.

Wannan jimilla ce ta tsawon watanni shida, ba wai za a biya ma’aikaci N420,000 lokaci guda ba.

5. Alawus ɗin ya bambanta da mafi ƙarancin albashi

Tallafin sufuri ba wani ɓangare ne na mafi ƙarancin albashi ba. A shekarar 2024, an ƙara mafi ƙarancin albashin ƙasa daga N30,000 zuwa N70,000.

Sai dai taron na baya-bayan nan bai warware saɓanin da ke tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago kan ranar fara aiwatar da wasu shirye-shiryen mafi ƙarancin albashin da ake tattaunawa a kai ba.

Kara karanta wannan

Wahalar rayuwa: Gwamnatin Tinubu ta ware N70,000 ga ma'aikata duk wata

Bangarorin sun amince da kafa kwamitin tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi, tare da fara zaman tattaunawa nan take.

6. Har yanzu ba a fayyace yadda za a biya kuɗin ba

Duk da cewa an bayyana adadin kuɗin, tsawon lokacin shirin da watan fara biyan su, ba a fayyace yadda za a gudanar da biyan ba.

Haka kuma, ba a bayyana ko ma’aikata za su cike takardar neman tallafin ba, hanyar da za a bi wajen biyan kuɗin ko kuma takamaiman rukunin ma’aikatan da za su amfana.

Ana buƙatar ƙarin bayani daga hukumomin da abin ya shafa domin warware waɗannan tambayoyi.

7. An ƙarfafa jihohi da ƙananan hukumomi su shiga shirin

Takardar yarjejeniyar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi su shiga shirin, yayin da aka bukaci ƙungiyoyin ƙwadago su matsa domin ganin an aiwatar da shi.

Sai dai yarjejeniyar ba ta tabbatar da cewa dukkan jihohi da ƙananan hukumomi sun amince da biyan tallafin ba.

Saboda haka, ma’aikatan da ba sa aiki a ƙarƙashin gwamnatin tarayya ya kamata su nemi ƙarin bayani daga gwamnatocinsu.

Kara karanta wannan

Kungiyar Amnesty ta shiga batun kisan Sheikh Masussuka a Katsina

8. Za a biya bashin wasu alawus-alawus

Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan basussukan alawus-alawus na musamman da ake bin ma’aikata, wanda ya fara daga ranar 1 ga Mayu, 2026.

An tsara fara biyan bashin a Nuwamba 2026, kuma za a raba kuɗin zuwa kashi uku daidai, a biya su cikin watanni uku.

Sai dai ba a bayyana jimillar bashin ko adadin kuɗin da kowane ma’aikaci zai samu ba.

9. Ma’aikatan lafiya za su samu wani tallafi na daban

Gwamnati ta amince da biyan ma’aikatan lafiya basussukan alawus na watanni 19 cikin watanni uku, daga Disamba 2026.

Haka kuma, an sa ran hukumar kula da albashi ta kasa za ta kammala nazarin kuɗin da ake buƙata domin gyara tsarin albashin ma’aikatan lafiya mai suna Consolidated Health Salary Structure cikin makonni uku.

Sai dai har yanzu ba a sanar da matsaya ta ƙarshe kan gyaran albashin ba, jaridar Leadership ta kawo labarin.

10. Akwai batutuwan jin daɗin ma’aikata da ba a warware ba

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Obi: Rigima ta kunno kai baya kafa kwamitin yakin neman zaben NDC

Yarjejeniyar ta kuma shafi alawus ɗin haɗarin aiki ga jami’an aikin gona da kuma shawarar rage haraji ga ma’aikata.

Ana tantance ma’aikatan aikin gona da za su amfana da kuɗaɗen da ake buƙata, kuma ana sa ran kammala aikin cikin makonni biyu.

A ɓangaren rage haraji kuwa, za a miƙa shawarar ga Majalisar Zartarwa ta Ƙasa domin ta duba ta.

Ana sa ran gwamnati da NLC za su sake zama bayan wata guda domin duba yadda ake aiwatar da yarjejeniyar da kuma ci gaban da aka samu wajen warware sauran matsalolin ma’aikata.

Za a fara biyan ma'aikata N70,000
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a wajen taron APC Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

NlC ta ba gwamnatin Tinubu wa'adi

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar kwadago ta NLC ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu ta rage farashin man fetur.

Kungiyar NLC ta yi gargadin cewa za ta dauki matakan da suka dace idan gwamnati ta gaza cika bukatunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng