Ana Wata Ga Wata: TUC Ta Kawo Cikas a Shirin Gwamnatin Tinubu na Fara Rabon Tallafin N70,000
- Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta yi watsi da tallafin sufuri na N70,000 da gwamnatin tarayya ta amince za ta biya ma'sikata duk wata
- Ƙungiyar ta bukaci a ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikatan tarayya daga N70,000 zuwa N300,000, tare da daidaita albashin sauran ma’aikata
- TUC ta kuma zargi gwamnati da kasa cika yarjejeniyar tallafin albashi na N40,000 da kuma rashin aiwatar da yarjejeniyarta da ƙungiyar ma’aikatan lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (TUC) ta yi watsi da tallafin sufuri na N70,000 da gwamnatin tarayya ta amince za ta rika biyan ma’aikata duk wata na wani lokaci.
Ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta ƙara albashinsu cikin gaggawa tare da cikakken aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da ƙungiyar haɗin gwiwar ma’aikatan lafiya ta JOHESU.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ceto mutane 70, sun kama ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi mutane a Arewa

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa matakin ƙungiyar ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan gwamnatin tarayya ta amince da tallafin sufuri.
TUC ta yi fatali da tallafin sufuri
Kungiyar TUC ta bayyana cewa tallafin albashi na wucin gadi bai isa ya magance matsin tattalin arzikin da ma’aikatan Najeriya ke fuskanta ba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Festus Osifo, da babban sakatarenta, Comrade N. A. Toro, suka sanya wa hannu.
TUC ta ce gwamnati za ta iya ƙara albashin ma’aikata ba tare da jiran kammala tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa ba.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ta gabatar da buƙatunta ga gwamnati a cikin wasiƙar ranar 8 ga Oktoba, 2026, bayan wani taron majalisar gudanarwarta ta ƙasa da aka gudanar a Abuja.
TUC ta nemi albashin N300,000
Ƙungiyar ta bayyana cewa babu wata doka da ta wajabta wa gwamnati sai ta kammala tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi kafin ta ƙara wa ma’aikata albashi.
TUC ta ba da shawarar cewa a ƙara mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya daga N70,000 da ake biya a yanzu zuwa N300,000, tare da yin daidaitattun ƙarin albashi ga ma’aikatan da ke sauran matakan albashi.
Ƙungiyar ta ce wasu jihohi sun riga sun ƙara mafi ƙarancin albashinsu zuwa sama da naira 100,000 saboda haka, ta yi imanin cewa gwamnatin tarayya ma za ta iya ƙara albashin ma’aikatanta mafi ƙaranci N300,000.
“Wasu jihohi a yau sun ƙara mafi ƙarancin albashinsu zuwa sama da N100,000. Don haka, gwamnatin tarayya za ta iya ƙara albashin ma’aikacinta mafi ƙaranci zuwa N300,000," in kmji TUC.

Source: Twitter
Bugu da ƙari, TUC ta zargi gwamnatin tarayya da kasa cika yarjejeniyarta da ƙungiyar haɗin gwiwar ma’aikatan lafiya ta JOHESU, duk da cewa ƙungiyoyin sun dakatar da yajin aikinsu watanni bakwai da suka gabata.
Gwamnati za ta duba batun karin albashi
Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta ce ta shirya dukkan matakan da suka dace domin fara tattaunawar sabon mafi karancin albashi.
Babban Sakataren Ma’aikatar Kwadago da Ayyukan yi ta Tarayya, Kamil Shoretire, ne ya bayyana hakan yayin wani taron yini guda da aka gudanar kan ayyukan ma’aikatar.
Asali: Legit.ng
