Wahalar Rayuwa: Gwamnatin Tinubu Ta Ware N70,000 ga Ma'aikata duk Wata

Wahalar Rayuwa: Gwamnatin Tinubu Ta Ware N70,000 ga Ma'aikata duk Wata

  • Gwamnatin Tarayya ta amince da ba ma’aikatan gwamnati tallafin sufuri na N70,000 duk wata na tsawon watanni shida,
  • Gwamnati ta amince da biyan bashin wasu alawus-alawus na ma’aikata daga 1 ga Mayun 2026, cikin kashi uku daidai, daga Nuwamba
  • Gwamnati da NLC sun kasa cimma matsaya kan ranar fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi, amma sun amince da fara tattaunawa nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta amince da ba ma’aikatan gwamnati a dukkan matakai tallafin sufuri na N70,000 duk wata na tsawon watanni shida, domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa.

Za a fara biyan tallafin ne daga watan Nuwamba na shekarar 2026, biyo bayan yarjejeniyar da gwamnati da shugabannin Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) suka cimma a Abuja ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta kawo dokar tattalin arziki da za ta yi aiki ko da ya sauka

Gwamnatin Tinubu za ta saukaka wa ma'aikata
Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Twitter

Gwamnatin Tinubu za ta saukaka wa ma'aikata

Wannan na daga cikin matakan da aka amince da su a taron sasanta rikici tsakanin gwamnati da ƙungiyar ƙwadago, bayan matsin lambar da ma’aikata suka yi kan tsadar rayuwa, walwalar ma’aikata da yarjejeniyoyin da ba a aiwatar ba, cewar Punch.

Gwamnatin ta kuma amince da biyan bashin wasu alawus-alawus na musamman na ma’aikata, daga ranar 1 ga Mayun 2026, cikin kashi uku daidai, inda za a fara biya daga Nuwamba.

Sai dai ɓangarorin biyu sun kasa cimma matsaya kan ranar fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa, duk da amincewa da kafa kwamitin tattaunawa nan take.

An bayyana waɗannan matsayai ne a cikin takardar fahimtar juna da aka sanya wa hannu bayan taron.

Yarjejeniyar tallafin sufuri

Ƙungiyoyin ƙwadago sun sha neman gwamnati ta ɗauki matakan rage wa ma’aikata matsin tattalin arziki, ciki har da rage farashin man fetur, ƙara albashi da aiwatar da yarjejeniyoyin jin daɗin ma’aikata da aka riga aka cimma, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Ana zargin yana tare da APC, Kwankwaso ya bada shawara kan sake zaɓen Tinubu a 2027

Game da tallafin sufuri, takardar ta bayyana cewa:

“An amince cewa za a biya tallafin sufuri na Naira dubu saba’in (N70,000), daga watan Nuwamba na 2026, ga ma’aikata a dukkan matakai na tsawon watanni shida.”

Sai dai takardar ba ta bayyana takamaiman ranar da za a riƙa biyan kuɗin a kowane wata ba, haka kuma ba ta fayyace tsarin gudanarwa da za a bi wajen raba tallafin ba.

Yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tsadar sufuri da farashin muhimman kayayyaki, bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023, matakin da ya taimaka wajen ƙara tsadar rayuwa a Najeriya.

Saɓani kan mafi ƙarancin albashi

Game da mafi ƙarancin albashi na ƙasa, ɓangarorin biyu sun amince cewa za a kafa kwamitin tattaunawa kan albashin, wanda zai fara gudanar da tarurruka nan take.

Sai dai ba a cimma matsaya kan ranar da za a fara aiwatar da shi ba.

Kara karanta wannan

Duk da ƙoƙarin Tinubu kan tsadar kaya, abinci na ci gaba da tashi a kasuwanni

Takardar ta ce:

“An amince cewa za a kafa Kwamitin Tattaunawa kan Mafi Ƙarancin Albashi, wanda zai fara gudanar da tarurruka nan take. Sai dai ya kamata a lura cewa akwai saɓani kan ranar fara aiwatar da shi.”

NLC na rigima da gwamantin Tinubu

An ji cewa kungiyar kwadago ta NLC ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu ta rage farashin man fetur tare da fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi.

NLC ta ce wa’adin zai fara ne daga Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026, tare da gargadin daukar matakan da suka dace idan gwamnati ta gaza cika bukatunta.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyoyin da ta cimma da ma’aikatan lafiya da sauran ma’aikatan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.