Atiku Ya Nuna Adawa da Shirin Tinubu na Tallafawa Ma'aikata da N70,000
- Atiku Abubakar ya soki tallafin sufuri na N70,000 da gwamnatin tarayya za ta bai wa ma’aikatan gwamnati na tsawon watanni shida
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce tallafin ba zai magance matsin tattalin arziki ba, yana tambayar sauran miliyoyin ’yan Najeriya
- Atiku ya bukaci gwamnati ta samar da tallafin man fetur da aka tace a Najeriya, yayin da ƙungiyar TUC ta nemi a ƙara albashin ma’aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki shirin gwamnatin tarayya na biyan ma’aikatan gwamnati tallafin sufuri na N70,000 duk wata.
Atiku ya bayyana cewa matakin wucin gadi ne da ba zai magance matsin tsadar rayuwa a Najeriya ba.

Source: Facebook
A wata sanarwa da Phrank Shaibu, daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya fitar ranar Laraba, cewar Vanguard.
Atiku ya soki shirin tallafawa ma'aikata kadai
Atiku ya ce kuɗin tallafin za su iya sayen kusan litar fetur 50 kacal, idan aka yi la’akari da farashin N1,400 kan kowace lita.
Ya ce shirin biyan tallafin na tsawon watanni shida yana nuna gazawar gwamnati wajen magance matsalolin tattalin arziki da suka addabi gidaje da kasuwanci.
Gwamnatin tarayya ta sanar da tallafin ne a cikin yarjejeniyar fahimtar juna da ta cimma da ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ranar Talata, inda aka tsara fara biyan kuɗin daga watan Nuwamba na 2026.
Yarjejeniyar ta biyo bayan makonni da aka kwashe ana takaddama tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago kan tsadar rayuwa, farashin fetur, jin daɗin ma’aikata da yarjejeniyoyin da ba a aiwatar ba.

Source: Facebook
Atiku ya kushe tsare-tsaren Tinubu a Najeriya
Atiku ya ce tallafin sufuri ba zai rage nauyin kuɗaɗen da ma’aikata da sauran ’yan Najeriya ke fuskanta ba, sakamakon ci gaba da tashin farashin kayayyaki da hidimomi.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: TUC ta kawo cikas a shirin gwamnatin Tinubu na fara rabon tallafin N70000
Ya ce:
“Matsalar tsadar rayuwa ta wuce batun sufuri. Kuɗin makamashi, abinci, haya da sauran muhimman buƙatu suna shafar kowane ɓangare na rayuwar yau da kullum.”
Ya yi nuni da hauhawar kuɗin samar da wutar lantarki ga kasuwanci, dafa abinci, tafiyar da motocin bas na makarantu da biyan kuɗaɗen kula da gidaje, yana tambayar ko gwamnati tana ganin matsalar ta tsaya ne a tashar mota.
Atiku ya kuma tambayi dalilin da ya sa aka takaita tallafin ga ma’aikatan gwamnati, alhali ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu, ’yan kasuwa, ƙananan sana’o’i, masu sufuri da ma’aikatan da ba sa cikin tsarin aikin gwamnati su ma suna fama da tsadar rayuwa.
Ya tambaya:
“Idan ma’aikatan gwamnati za su riƙa samun N70,000 na sufuri duk wata daga Nuwamba, me zai faru da ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu, ’yan kasuwa, ƙananan ’yan kasuwa, masu sufuri da miliyoyin mutanen da ba su da ayyukan yi na yau da kullum?”
Ya bayyana tallafin na tsawon watanni shida a matsayin wanda bai wadatar ba, yana mai cewa biyan kuɗi na ɗan lokaci ba zai iya sauya illolin manufofin tattalin arzikin gwamnati ba.
NDC ta caccaki Atiku Abubakar
An ji cewa daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na NDC, Ibrahim Abdulkarim, ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya haɗa kai da Peter Obi.
Abdulkarim ya ce Kwankwaso ya ajiye burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa domin aiki tare da Obi, yana mai cewa sauran shugabannin hamayya suna da damar shiga haɗakar.
Ya kuma yi alƙawarin cewa NDC za ta kare ƙuri’un masu zaɓe a 2027, tare da cewa Obi zai zaɓi ƙwararrun mutane bisa cancanta idan ya zama shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng

