Shettima Ya Sanar da Shirin Raba Miliyoyin Buhunan Taki ga Masu Noman Rani
- Kashim Shettima ya umarci hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki su gaggauta samar da buhunan taki sama da miliyan 3
- Gwamnatin tarayya na shirin sayen takin da kamfanonin cikin gida suka samar domin sayar wa manoma kan farashi mai sauƙi
- Shettima ya kuma umarci jami’an tsaro da su tabbatar da adalci wajen rabon takin, musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya umarci hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki a masana’antar takin zamani da su gaggauta shirye-shiryen samar da buhunan takin sama da miliyan 3.
Rahotanni sun bayyana cewa za a taadi takin ne domin rabawa manoma a faɗin Najeriya gabanin fara noman rani.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Gobara ta kama a katafariyar ma'ajiyar babban dan kasuwa a jihar Kaduna

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa Umarnin ya biyo bayan amincewar Shugaba Bola Tinubu da samar da kuɗi ƙarƙashin shirin noma na Renewed Hope da aka ƙirƙira domin rage tsadar takin zamani, ƙara yawan amfanin gona da farfaɗo da masana’antun taki.
Takin da ake so a samar
A yayin taron, ƙungiyar masu samarwa da sayar da takin zamani ta Najeriya (FEPSAN) ta bayyana cewa akwai isassun kayan haɗa takin da za su iya samar da buhunan takin NPK kusan miliyan uku cikin makonni masu zuwa.
Mataimakin shugaban kasar ya kuma umarci Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA) da ya tantance tare da sanya ido kan adadin takin da masu ruwa da tsaki suka bayyana cewa suna da shi.
Ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana, tare da sauƙaƙa rabon takin ga manoma.
Yadda za a raba takin
Shettima ya kuma buƙaci ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro da ya tabbatar da cewa manoman da ke yankunan da ke fuskantar matsalar tsaro ba a bar su a baya ba.
Ya jaddada muhimmancin kai tallafin ga manoman da ke yankunan da ke da nisa, musamman waɗanda ke cikin mawuyacin hali saboda matsalolin tsaro.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce farfaɗo da masana’antar takin zamani zai ƙara bunƙasa noma, samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar al’ummomin karkara.

Source: Getty Images
Baun farfado da masana'antu
Shettima ya nuna damuwa kan yadda masana’antun haɗa takin zamani da dama a Najeriya ke aiki ƙasa da ƙarfinsu, duk da yadda buƙatar takin mai sauƙin farashi ke ƙaruwa.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu na son farfaɗo da waɗannan masana’antu domin su koma aiki yadda ya kamata, ma’aikata su koma bakin aikinsu, sannan masu jigilar kaya, masu ajiya da dillalan kayan noma su samu ayyukan yi.
Shettima ya jaddada cewa manoman Najeriya ne za su fi amfana da shirin, domin gwamnati za ta sayi takin da kamfanonin cikin gida suka samar, sannan ta samar da shi ga manoma kan farashi mai sauƙi.
Ga bidiyon da Shettima ya yi bayani a kasa:
Sule Lamido ya soki Shettima
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya musanta ikirarin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi na cewa yana goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki.
Sule Lamido ya bayyana mamakinsa kan yadda za a ce ya koma APC, alhali bai taɓa goyon bayan jam’iyyar ba tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2014.
Tsohon gwamnan ya yi amfani da kalmar Kanuri ta “kattuwunum”, wadda ke nufin ƙarya ce, wajen wulakanta ikirarin Shettima, tare da fitar da bayanin wani magoya bayansa.
Asali: Legit.ng

