Abdul Samad Rabiu Ya Faɗi Ribar da Ya Samu saboda Tsare Tsaren Tinubu

Abdul Samad Rabiu Ya Faɗi Ribar da Ya Samu saboda Tsare Tsaren Tinubu

  • Dan kasuwa Abdul Samad Rabiu ya ce gyare-gyaren tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu sun fara ƙara kwarin gwiwar masu zuba jari a Najeriya
  • Attajirin ya bayyana cewa kamfanoninsa na ɓangaren abinci da siminti sun kai darajar kasuwa sama da dala biliyan 17, sakamakon bunƙasar kasuwancinsu
  • Rabiu ya buƙaci gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu su samar da ƙarin manyan kamfanonin masana'antu 100 domin bunƙasa tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya magantu kan tsare-tsaren Bola Tinubu.

Abdul Samad ya bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu sun fara ƙara kwarin gwiwar masu zuba jari a Najeriya.

Abdul Samad ya yabawa salon mulkin Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da attajiri, Abdul Samad Rabi'u a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne a cikin jawabin buɗe taron da ya gabatar a taron koli na tattalin arzikin Najeriya karo na 32, wanda aka gudanar ranar Talata a Abuja, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Taimakon da gwamnatin Tinubu ta nema kan shirin yan sanda jihohi a Najeriya

Bukatar Abdul Samad ga kamfanoni

Attajirin ya buƙaci gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu su samar da aƙalla ƙarin manyan kamfanonin masana'antu 100 na 'yan Najeriya domin haɓaka samar da kayayyaki, samar da ayyukan yi da ƙarfafa tattalin arziki.

Dan kasuwr ya ce gyare-gyaren da ake yi dole ne su haifar da ƙarin samar da kayayyaki, damar ayyukan yi da inganta rayuwar jama'a.

Ya yaba da ingantuwar samun kuɗin musayar waje, inda ya tuna da wahalhalun da kamfanoni suka sha a baya wajen samun daloli don sayen injuna, kayan aiki da albarkatun ƙasa, duk da suna da isassun kuɗin naira.

Ya ce:

“Yanzu kamfanonin da ke gudanar da halastattun harkoki za su iya samun kuɗin musayar waje ta kasuwa bisa farashin da ake amfani da shi, maimakon dogaro da rabon kuɗin kai tsaye daga Babban Bankin Najeriya.”

Ya bayyana cewa ingantuwar tsarin samun kuɗin musayar waje ta sa tsara jarin kasuwanci ya fi sauƙi da tabbas, musamman ga masana'antun da ke gudanar da manyan ayyuka.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ɗan agajin Izala kan zargin barazana ga Kiristoci a bidiyo

An yaba wa Tinubu kan sauyi a tattalin arziki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Twitter

Attajirin ya ce tun bayan da Olayemi Cardoso ya zama gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), sau kaɗan kawai ya gana da shi, sabanin lokacin baya da 'yan kasuwa ke yawan zuwa bankin neman rabon kuɗin musayar waje.

Shawarar Abdul Samad ga gwamnati

Duk da amincewa da matsalolin da iyalai da kamfanoni ke fuskanta, Rabiu ya buƙaci gwamnati ta ci gaba da gyare-gyaren tare da ba da fifiko ga faɗaɗa ƙarfin samar da kayayyaki a Najeriya.

Ya ce:

“Dole ne mu wuce daga gyare-gyare zuwa sakamako, daga daidaita tattalin arziki zuwa faɗaɗa shi, sannan daga sauye-sauyen tattalin arziki zuwa wadata da kowa zai amfana da ita.”

Da yake bayyana ci gaban rukunin BUA, Abdul Samad Rabiu ya ce kamfanonin BUA Foods da BUA Cement, waɗanda aka jera a kasuwar hannayen jari ta Najeriya, sun kai darajar kasuwa ta haɗin gwiwa sama da dala biliyan 17.

Ya bayyana cewa darajar BUA Foods ta haura dala biliyan 10, yayin da BUA Cement ta kai kusan dala biliyan 7, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Obi ya bukaci Bola Tinubu ya koma gida ya huta, ya bar maganar takarar 2027

Uba Sani zai sayar da rai saboda Tinubu

An ji cewa Uba Sani ya ce ba zai yi nadamar goyon bayan Tinubu ba, kuma zai ci gaba da mara masa baya har zuwa ƙarshen lokacin yaƙin neman zaɓe.

Gwamnan ya danganta goyon bayansa ga alaƙar siyasa da ke tsakaninsu tun shekarar 1994, lokacin gwagwarmayar dawo da mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.

Ya ce amincewa da wasu manyan ayyukan jami'o'i da gyaran hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari na daga cikin abubuwan da suka amfani jihar a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.