Tinubu Ya Nemi Izinin Sake Karbo Bashi Kala 2 da Ya Kai Kusan N30trn daga Kasashen Waje

Tinubu Ya Nemi Izinin Sake Karbo Bashi Kala 2 da Ya Kai Kusan N30trn daga Kasashen Waje

  • Shugaba Bola Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin Najeriya ta ciwo bashin Dala biliyan 20.51 da Yuro biliyan 1.45 daga ƙasashen waje
  • Ya ce bashin zai taimaka wa gwamnatin tarayya wajen cike gibin kuɗaɗen da ake buƙata a ƙarin kasafin kuɗin 2026 zuwa 2027
  • Majalisar Dattawa ta miƙa buƙatar ga kwamitocin da abin ya shafa, waɗanda aka ba wa mako guda su gabatar da rahoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin ciwo bashin Dala biliyan 20.51 da Yuro biliyan 1.45 daga ƙasashen waje.

Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da wadannan kudi ne domin cike gibin kuɗaɗen da ake buƙata a kasafin kuɗin gwamnatin tarayya na shekarar 2026 zuwa 2027.

Kara karanta wannan

"Ba zai yiwu mu koma baya ba," Gwamna ya yi fatali da yunkurin dawo da tallafin Fetur

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ofishinsa da ke fadar Aso Rock, Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Shugaban ƙasar ya gabatar da buƙatar ne a cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman majalisar ranar Talata.

A cikin wasiƙar, Tinubu ya bayyana cewa amincewa da shirin karbo bashin zai bai wa gwamnatin tarayya damar sauke nauyin da ke kanta ga ’yan Najeriya tare da samar da kuɗaɗen gudanar da muhimman ayyuka a sassa daban-daban.

Dalilin neman sabon bashin

A cikin wasiƙar, Tinubu ya ce:

“Na hado wannan wasika da cikakken bayanin shirin da muka yi na ciwo bashin kuɗaɗen waje na shekarar 2026 zuwa 2027 domin Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta duba shi tare da amincewa da shi cikin gaggawa, don tabbatar da fara aiwatar da ayyukanmu a kan lokaci.”

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa an tsara shirye-shiryen da ke cikin wannan tsari ne bisa nazarin fasaha da tattalin arziki, tare da yin la’akari da gudummawar da ake sa ran za su bayar wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da ci gaban al’umma.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano masu shirya kai farmaki kan matasan da za su y aikin zaɓen 2027

Ya ce an tsara shirye-shiryen ne domin samar da ayyukan yi, bunƙasa koyon sana’o’i da kasuwanci, rage talauci da kuma inganta wadatar abinci a ƙasar.

Majalisa ta tura buƙatar ga kwamitoci

Da yake magana kan buƙatar, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa an riga an tattauna wasu ɓangarorin shirin ciwo bashin a baya yayin nazarin kasafin kuɗi.

Ya kuma ce an taɓa amincewa da wani shirin ciwo bashin daga ƙasashen waje a wani lokaci da ya gabata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Senate.
Shugaban Majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akabio yana jagorantar zama a Abuja Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Sanata Akpabio ya miƙa buƙatar ga Kwamitin Majalisar Dattawa kan Basussukan Cikin Gida da na Ƙasashen Waje, tare da haɗin gwiwar kwamitocin kasafin kuɗi da kuɗi.

Ana sa ran kwamitocin za su kammala nazarin buƙatar tare da gabatar da rahotonsu ga Majalisar Dattawa cikin mako guda.

Najeriya za ta karbi bashi daga China

Kun ji cewa Najeriya ta fara tattaunawa da bankin safarar kayayyaki na kasar China watau China Exim Bank domin karbo rancen Dala biliyan 2.

Gwamnatin Najeriya na kokarin karbo wannan bashi ne domin gina tashar wuta ta musamman da nufin share hawayen 'yan Najeriya game da karancin hasken lantarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262