An Bayyana Mutanen da aka Kama bayan Kai wa Kwankwaso Hari a Kano

An Bayyana Mutanen da aka Kama bayan Kai wa Kwankwaso Hari a Kano

  • Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama mutum takwas bayan rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan APC da NDC a karamar hukumar Bichi
  • Rahotannin da Legit ta samu sun ce rikicin ya yi sanadin jikkatar mutane biyar tare da lalata motoci 13 da fastocin yakin neman zabe
  • Biyo bayan lamarin, dakarun ’yan sanda sun kwato adduna biyu, sanduna biyu da wasu abubuwa daga hannun wadanda ake zargin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama mutum takwas bayan wani rikici da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC da NDC a karamar hukumar Bichi.

Rikicin ya faru ne ranar Lahadi, inda mutane biyar suka jikkata, yayin da aka lalata motoci 13 da fastocin yakin neman zabe da allunan tallan siyasa.

Kara karanta wannan

An rasa rai bayan rikici ya ɓarke tsakanin makiyaya da tawagar kamfen siyasa

Yan daban da aka kama a Kano
Mutane 8 da aka kama a Kano bayan rikici siyasa. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a Facebook, inda ya ce jami’an tsaro sun kwato wasu makamai da abubuwa daga hannun wadanda ake zargin.

’Yan sanda sun kwato makamai

Kiyawa ya ce jami’an tsaro sun kwato adduna biyu, sanduna biyu, garuyo guda daya, kwalbar wani sinadari da kuma wani abu da aka fi sani da suna “Suck and Die”.

Ya bayyana cewa an tura wadanda aka kama zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na rundunar, SCID, da ke Bompai domin gudanar da bincike.

Punch ta wallafa cewa kakakin rundunar ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

An dawo da zaman lafiya a Bichi

Kiyawa ya ce rundunar ta tura jami’an tsaro zuwa yankin, lamarin da ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kwamishinan ’yan sandan jihar ya yi Allah wadai da rikicin, yana mai gargadin magoya bayan siyasa da su guji duk wani abu da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma.

Kara karanta wannan

'An jikkata mutane da dama a harin da aka kai wa Kwankwaso a Kano,' Obi

Ya kuma bukaci ’yan siyasa da magoya bayansu su gudanar da harkokin siyasa cikin lumana tare da bin doka.

Kwankwasiyya ta soki gwamnatin Kano

A wani bangare kuma, kungiyar Kwankwasiyya ta soki gwamnatin jihar Kano bisa musanta zargin kai hari kan ayarin motocin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a karamar hukumar Bichi.

Mai magana da yawun kungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, 2026.

Abdullahi Haruna Kiyawa
Kakakin 'yan sandan jihar Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Sanarwar ta biyo bayan rahotannin cewa an kai wa ayarin motocin Kwankwaso hari yayin wasu ayyukan siyasa a Bichi ranar Lahadi, 15 ga Nuwamba.

Maganar da Kwanwkaso ya yi

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin dan takarar shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bukaci magoya bayansa a Bichi da su kasance cikin shirin tunkarar duk wani kalubale.

Kwankwaso ya yi wannan kira ne yayin wani gangamin yakin neman zabe a karamar hukumar Bichi, kwanaki bayan kungiyar Kwankwasiyya ta yi zargin cewa wasu ’yan daba sun kai hari kan ayarin motocinsa.

Tsohon gwamnan na Kano ya kuma shawarci magoya bayansa da su yi amfani da dabarar kwanton bauna wajen tunkarar duk wanda ya kalubalance su a karamar hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng