Isa Ashiru Ya Fito da Gaskiyar Zance bisa Zargin Ya Fallasa El Rufai kan Rashin Tsaro a Kaduna
- Isa Mohammed Ashiru ya musanta rahoton da ke cewa ya zargi tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da haddasa taɓarɓarewar tsaro a jihar
- Ɗan takarar na ADC ya ce an karkatar da ma’anar kalamansa ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin
- Isa Ashiru ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su tabbatar da sahihancin rahotanninsu, musamman kan batutuwan siyasa masu muhimmanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Ɗan takarar gwamnan Kaduna na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Rt. Hon. Isa Mohammed Ashiru, ya yi martani kan zargin cewa ya dora alhaki ga Nasir El-Rufai kan tabarbarewar tsaro a jihar.
Isa Ashiru Kudan ya musanta zargin cewa ya ɗora wa tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, alhakin ƙaruwa da taɓarɓarewar matsalar tsaro a Kaduna.

Source: Facebook
Isa Ashiru ya ce an karkatar da kalamansa
Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Abdulwaheed Olayinka Adubi, ya fitar a madadinsa.
A cikin sanarwar, Isa Ashiru ya bayyana rahoton a matsayin wanda ya ba da bayanin da bai dace da matsayinsa ba.
Ya ce an fahimci kalaman da ya yi yayin wata hira da gidan talabijin ta wata hanya dabam, sannan aka gabatar da su ga jama’a ba tare da kiyaye ainihin abin da ya faɗa ba.
Isa Ashiru ya jaddada cewa rahoton bai bayyana ainihin matsayarsa game da tsohon gwamnan ko ƙalubalen tsaron da jihar ke fuskanta ba.
Ya bukaci a gyara rahoton yadda ya dace
Ɗan takarar na ADC ya bayyana kwarin gwiwar cewa za a ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa rahoton da aka wallafa ya yi daidai da abin da aka tattauna a hirar da kuma yanayin da aka yi maganganun.
Isa Ashiru ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su riƙa tabbatar da cewa rahotannin hirarraki da sauran abubuwan da suka shafi jama’a suna bayyana ainihin ra’ayoyin waɗanda aka yi magana da su.
Ya ce rahotannin da suka karkatar da ma’anar kalaman mutane na iya sa jama’a su fahimci al’amura ba daidai ba, tare da kawo cikas ga tattaunawar siyasa mai amfani a tsarin dimokuraɗiyya.
Isa Ashiru ya yi kira ga 'yan jarida
Isa Ashiru ya sake bayyana girmamawarsa ga kafafen yaɗa labarai, yana mai cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da riƙon amana, ƙarfafa dimokuraɗiyya da sanar da jama’a abubuwan da ke faruwa.
Duk da haka, ya yi kira ga ’yan jarida da sauran masu aikin yaɗa labarai da su kiyaye ƙa’idojin ƙwarewa, sahihanci da yin cikakken bincike kafin wallafa rahotanni.
Ya ce wannan ya fi zama wajibi musamman wajen rahotannin da suka shafi batutuwan siyasa masu muhimmanci, inda kuskuren gabatar da kalamai zai iya haifar da ruɗani a tsakanin jama’a.

Source: Facebook
Kotu ta yi watsi da bukatar El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa kotu ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na cewa babu isassun hujjojin da za su sa a bukaci ya kare kansa.
Kotun ta yi watsi da bukatar ne a shari’ar da ake yi masa kan zargin kutse ba bisa ka’ida ba a bayanan kiran waya.
Asali: Legit.ng

