El Rufai Ya San Matsayarsa da kotu Ta Yanke Hukunci kan Karar da Ya Shigar kan DSS

El Rufai Ya San Matsayarsa da kotu Ta Yanke Hukunci kan Karar da Ya Shigar kan DSS

  • Mai shari’a Sylvanus Oriji ya yi watsi da ƙarar Naira miliyan 120 da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar kan DSS da wasu hukumomi
  • Kotun ta ce wasiƙun gayyatar da EFCC da ICPC suka aika wa El-Rufai domin bincike ba su keta haƙƙoƙinsa na asali ba
  • Alƙalin ya umarci El-Rufai ya biya kowanne daga cikin waɗanda ake ƙara Naira 200,000 a matsayin kuɗin shari’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai shari’a Sylvanus Oriji na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) ya yi watsi da ƙarar take haƙƙoƙin ɗan Adam ta Naira miliyan 120 da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar kan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da wasu hukumomi uku.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Oriji ya ce ƙarar ba ta da ingantaccen tushe ko hujjojin da za su sa kotu ta amince da ita.

Kara karanta wannan

An kai maganar barazana kan rayuwar Atiku gaban Shugaba Trump

Kotu ta yi watsi da karar El-Rufai
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

Alƙalin ya kuma umarci El-Rufai ya biya kowanne daga cikin waɗanda ake ƙara Naira 200,000 a matsayin kuɗin shari’a, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Abin da kotu ta ce kan wasiƙun gayyatar bincike

Kotun ta bayyana cewa wasiƙun gayyatar da hukumomin gwamnatin tarayya biyu suka aika wa El-Rufai domin ya bayyana a gaban su kan zarge-zargen da ake yi masa sun cika ƙa’idojin kundin tsarin mulki.

A cewar kotun, wasiƙun ba su keta haƙƙoƙin ɗan Adam na asali ba.

Musamman, Mai shari’a Oriji ya ce hukumomin EFCC da ICPC ba su take haƙƙin El-Rufai ba ta hanyar aika masa wasiƙun gayyata domin ya yi bayani kan batutuwan da aka gabatar a kansa.

Kotu ta goyi bayan ikon DSS

Dangane da yunƙurin kama El-Rufai da DSS ta yi a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, kotun ta amince da bayanin DSS cewa doka ta ba ta ikon sanya mutane cikin jerin waɗanda take sa ido a kansu da kuma kama waɗanda take buƙatar bincika.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An maka INEC kara gaban kotu kan N126bn

Kotun ta kuma bayyana cewa El-Rufai ba zai iya amfani da kotu wajen hana hukumomin gwamnati gudanar da ayyukan da doka ta ba su ba.

Mai shari’a Oriji ya yi watsi da hujjar El-Rufai cewa ba a samu takardar izinin kama shi ba kafin yunƙurin kama shi, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

Alƙalin ya ce DSS tana da wasu daga cikin ikon da ’yan sanda suke da su bisa tanade-tanaden dokokin da suka kafa hukumar tsaro ta farin kaya da kuma dokar mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro.

Kotu ta ce karɓe fasfo ɗinsa ya halatta

Dangane da zargin cewa DSS ta take haƙƙin El-Rufai ta hanyar ƙwace fasfo ɗinsa, kotun ta ce ta gamsu cewa an yi hakan ne bisa doka da kuma ikon da aka ba hukumar.

Kotun ta ƙara da cewa El-Rufai bai gabatar da hujjojin da za su tabbatar da cewa ƙwace fasfon ya ci gaba har abada, ya zama na dindindin ko kuma an yi shi ba bisa doka ba. Saboda haka, kotun ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan ya shigar.

Kara karanta wannan

An hura wa Tinubu wuta kan 2027, ana so ya hakura da shiga takara

Kotu ta ki amincewa da bukatar El-Rufai
Malam Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Kotu ta yi watsi da bukatar El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun daukaka kara da ke zamanta a Kaduna ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya shigar domin ƙalubalantar hukuncin Babbar Kotun jihar Kaduna na hana shi beli.

A hukuncin da ta yanke kan ƙara mai lamba CA/K/254C/2026, kotun ta tabbatar da hukuncin kotun ƙasa wanda ya ahana ba fa belin Malam Nasir El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng