Bayan Murabus a Gwamnatin Tinubu, INEC Ta Saka Sunan Tsohon Minista Ya Yi Takara
- Hukumar INEC ta sanya sunan tsohon ministan kimiyya da fasaha da ya murabus cikin jerin ’yan takarar gwamnan Enugu a zaɓen 2027
- Tsohon ministan ya yi murabus daga muƙaminsa a shekarar 2025 bayan zargin amfani da takardun shaidar karatu na bogi
- Dan takarar PDP ya gabatar da sakamakon WAEC maimakon digirin da ake takaddama a kai, yayin da yake fuskantar shari’ar gurfanarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta saka sunan tsohon minista da ta yi murabus a jerin yan takara.
Hukumar ta amince da Geoffrey Nnaji, tsohon ministan kimiyya da fasaha, ya tsaya takarar gwamnan Enugu a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Nnaji ya shiga cikin ƴan takara
Rahoton Daily Trust ya ce Nnaji ya yi murabus daga muƙaminsa bayan zargin mallakar da takardun bogi.
Ana zargin ya gabatar da shaidar karatu da na NYSC na bogi ga Shugaba Bola Tinubu da Majalisar Dattawa a lokacin tantance shi a shekarar 2023.
Rahoton ya yi zargin cewa Jami’ar Najeriya ta Nsukka (UNN) ta musanta bayar da takardar shaidar digirin da Nnaji ya gabatar, tana mai cewa an ba shi gurbin karatu a shekarar 1981, amma bai kammala karatunsa ba kuma ba a ba shi digiri ba.
Binciken ya kuma bayyana cewa a cikin wata takardar rantsuwa da aka gabatar a kotu, Nnaji ya amince cewa jami’ar ba ta taɓa ba shi takardar shaidar digiri ba, kuma ya ce bai taɓa karɓar irin wannan takarda ba.

Source: Facebook
INEC ta saka sunan Nnaji da takardar WAEC
An sanya sunan Nnaji a matsayi na 13 cikin jerin sunayen ’yan takarar da hukumar ta fitar a daren ranar Asabar.
A cewar jerin sunayen da sakatariyar INEC, Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP bai gabatar da digirin da ake takaddama a kai ba, sai dai ya gabatar da sakamakon jarabawar WAEC.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffuka Masu Alaƙa da Ita (ICPC) ta kama Nnaji a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, ranar 1 ga Yuli, 2026.
A cewar hukumar, kama shi ya biyo bayan ƙin amsa gayyata da dama da aka aika masa.
Daga baya aka gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zargin yin jabun takardar shaidar karatu, amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida ba da kuma halatta kuɗin haram.
Nnaji ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa da su, sannan kotu ta bayar da belinsa kan kuɗin naira miliyan 20 tare da mutum ɗaya da zai tsaya masa.
An cire sunan Pantami a cikin ƴan takara
An ji cewa sunan tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, bai bayyana a jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar gwamnan Gombe ba.
Hukumar INEC ta amince da ’yan takara 16 domin fafatawa a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
Kotun Ƙoli ta dawo da wasu sassan Dokar Zaɓe ta 2026 da suka hana jam’iyyu tsayar da ’yan takarar da sunayensu ba sa cikin rajistar mambobin da aka miƙa wa INEC.
Asali: Legit.ng

