Najeriya Ta Yi Rashi: 'Yan Boko Haram Sun Hallaka Kwamandan Jami'an Tsaro

Najeriya Ta Yi Rashi: 'Yan Boko Haram Sun Hallaka Kwamandan Jami'an Tsaro

  • Yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun kai hari Wumbi a ƙaramar hukumar Kala-Balge, inda suka kashe kwamandan ’yan banga da fararen hula huɗu
  • Kwamandan ya tsaya ya tunkari maharan domin bai wa manoma damar tserewa, amma daga bisani aka kashe shi
  • Dan takarar kujerar majalisa ta Bama/Kala-Balge/Ngala ya kai ziyara domin jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP ne sun kai wani mummunan hari kan al’ummar Wumbi da ke ƙaramar hukumar Kala-Balge a Jihar Borno.

Rahotanni sun ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar wani kwamandan ’yan sa-kai da fararen hula huɗu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

'Yan Boko Haram sun kai hari a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ce kauyen Wumbi wani gari da a ke noma kuma yake iyaka da Jamhuriyar kasar Kamaru

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali da 'yan bindiga suka kashe mataimakin kwamandan rundunar tsaro a Plateau

A baya, mazauna yankin sun bar garin sakamakon yawan hare-haren ’yan ta’adda. Sai dai a baya-bayan nan, wasu mazauna yankin sun fara komawa domin noma gonakinsu, ƙarƙashin kariyar Civilian Joint Task Force (CJTF) da ’yan sa-kai.

Kwamandan ya tsaya domin kare manoma

Majiyoyi sun ce a daren Laraba ne ’yan ta’addan suka shirya kai harin, inda suka zo da dimbin mutane da nufin kai wa kwamandan ’yan sa-kan hari.

An ce kwamandan ya kasance babban cikas ga ayyukan ’yan ta’addan a yankin, lamarin da ya sa suka mayar da hankali wajen kai masa farmaki.

A lokacin da aka kai harin, mafi yawan manoman da ke yankin sun samu damar tserewa.

Sai dai kwamandan ya tsaya a baya domin tunkarar maharan da kuma ba sauran manoman damar tserewa.

An kashe kwamandan bayan artabu

Wani ɗan banga da ya yi magana da sharadin sakaya sunansa ya ce maharan sun fi kwamandan yawa, inda daga bisani suka samu nasarar rinjayarsa.

Kara karanta wannan

Karya ta ƙare: Yan bindiga sun ga bala'in da ya fi ƙarfinsu, kusan 20 sun bakunci lahira

A cewar majiyar, bayan sun fahimci cewa harbin bindiga bai iya cutar da shi ba saboda kayan kariya da yake amfani da su, maharan sun sauya dabara.

Ya ce daga bisani sun kashe kwamandan ta hanyar karya masa wuya.

Bam ya kashe wasu yayin dauke gawar

Majiyar ta ce bala’in ya ƙara muni lokacin da wasu daga cikin jama'a da jami’an tsaro suka taru domin dauke gawar kwamandan.

Ya bayyana cewa an binne abubuwan fashewa a ƙarƙashin gawar kwamandan.

“Yayin da suka kusanci gawar, IED da aka binne a ƙarƙashinta suka tashi, inda suka kashe wasu mutane huɗu tare da jikkata wasu ’yan banga, CJTF da fararen hula,” in ji majiyar.

’Yan sanda sun tabbatar da harin

Mai magana da yawun rundunar, ASP Kenneth Daso, ya ce kwamandan ’yan bangan da wasu mutane huɗu sun rasa rayukansu yayin arangamar da aka yi da ’yan ta’addan.

Ya ce bayanan farko da rundunar ta samu har yanzu ba su cika ba, amma za a fitar da ƙarin bayani da zarar an samu cikakkun bayanai.

Dan takarar APC ya jajanta

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Obi sun samu babbar dama a kwamitin yakin neman zaben NDC

Hon. Mustapha Babani, ɗan takarar APC na mazabar tarayya ta Bama/Ngala/Kala-Balge, ya ziyarci yankin domin jajanta wa iyalan waɗanda harin ya shafa.

Ya kai ziyarar ne domin nuna alhini da ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a harin.

'Yan Boko Haram sun kashe kwamanda a Borno
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan Boko Haram sun kashe mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa yan ta’addan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Bitirhuya da ke ƙaramar hukumar Hong a jihar Adamawa,

Hatsabiban 'yan ta'addan wadanda ke dauje da makamai sun kashe mazauna yankin huɗu tare da ƙona gidaje da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng