Sarki Sanusi Ya Dawo da Tsohuwar Magana, Ya Roki Abba Kabir Alfarma a Kano
- Sarki Muhammadu Sanusi II ya roƙi Gwamnatin Kano ta biya diyya ga ’yan kasuwar da rusau ya shafa
- Mai Martaba ya rubuta wa Gwamna Abba Yusuf wasiƙa, yana neman a tallafa wa ’yan kasuwar da rusau ya jefa cikin matsanancin hali
- Wani farfesa ya buƙaci gwamnati ta gina sabuwar kasuwa ta zamani, yana mai cewa kasuwar na tallafa wa mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya tura alfarma ta musamman ga Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir.
Sarkin ya bukace shi da ya biya diyya ga ’yan kasuwar da rusau ya shafa a kasuwar Filin Idi, da ke Kofar Mata, Kano, tare da sake ware musu wuraren kasuwanci domin su ci gaba da sana’o’insu.

Source: Facebook
Sanusi, wanda Ibrahim Mai Bushira ya wakilta, ya yi wannan kira ne a wani zaman addu’a na musamman da ’yan kasuwar da rusau ya shafa suka shirya, cewar Channels TV.
Dalilin Sanusi na rubuta wa Abba wasika
A cewar Mai Bushira, Sanusi ya rubuta wasiƙa ga Gwamna Abba Yusuf, yana neman a biya ’yan kasuwar diyya tare da ɗaukar matakan da za su rage asarar tattalin arzikin da suka yi sakamakon rusau ɗin.
Ya bayyana fatansa na cewa Allah Maɗaukakin Sarki zai saka wa Emir da alheri bisa wannan shiga tsakani da ya yi, sannan ya buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi la’akari da buƙatun ’yan kasuwar domin su sake gina sana’o’insu da dawo da hanyoyin samun abin rayuwarsu.
Mai Bushira ya ce rusau ɗin ya jefa ’yan kasuwar cikin matsanancin hali, musamman ganin cewa da yawa daga cikinsu sun dogara da shagunan a matsayin babbar hanyar samun kuɗin shiga.
Ya ƙara da cewa an ruwaito cewa wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun rasu, yayin da wasu suka kamu da hawan jini sakamakon rusa sana’o’insu da matsalolin tattalin arzikin da suka biyo baya.
Sannan ya bayyana cewa an shirya zaman addu’ar ne domin neman taimakon Allah kan halin da suke ciki da kuma roƙon dawo da hanyoyin samun abin rayuwarsu.
Mai Bushira ya kara da cewa rushe shagunan ya shafi rayuwar iyalai da dama waɗanda suka dogara da kasuwar wajen samun abin da za su ci.

Source: Twitter
An buƙaci gwamnati ta kula da halin ’yan kasuwar
Da yake jawabi a wurin taron, Ahmad Muhammad na Jami’ar Tarayya da ke Dutse (FUD), ya bayyana Kano a matsayin babbar cibiyar kasuwanci, tare da kira ga Gwamnatin Kano da ta kula da halin da ’yan kasuwar ke ciki da illolin tattalin arzikin da rusau ɗin ya haifar.
Muhammad ya kuma roƙi ’yan kasuwa da masu zuba jari na ƙasashen waje da su binciki hanyoyin tallafa wa ci gaban kasuwar, yana mai jaddada cewa rushe shagunan ya jawo asarar kuɗi mai yawa da ta kai biliyoyin nairori.
Ya buƙaci gwamnati ta yi la’akari da gina sabuwar kasuwa ta zamani a wurin, yana mai cewa kasuwar Filin Idi ba cibiyar kasuwanci ce ta Kano kaɗai ba, domin tana da muhimmanci ga ’yan kasuwa daga sassa daban-daban na Najeriya da kuma faɗin Afirka.
Sanusi II ya magantu kan zaluntar El-Rufai
Mun ba ku labarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce mutum na iya aikata kusan komai a Najeriya ya kuɓuta idan yana da alaƙar siyasa mai ƙarfi.
Sanusi II ya ce akwai hukumomi da kotuna da aka kafa domin yaƙi da cin hanci, amma yadda ake aiwatar da dokokin na iya fuskantar tasirin siyasa.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma matsalar dukiyar da ba a iya bayyana tushenta ba.
Asali: Legit.ng


