Samaila Kaigama Ya Fara Fuskantar Hukunci kan Zargin Taimaka Wa Yan Ta'adda a Najeriya
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Samaila Kaigama a gidan gyaran hali na Kuje bisa zargin alaƙa da ta'addanci
- Ana zargin Kaigama da taimaka wa ISWAP ta hanyar shiga tattunawar kuɗin fansa da kuma karɓar kuɗaɗen daga iyalan waɗanda aka sace
- Kotu ta sanya ranar 13 ga Nuwamba domin fara shari'ar, yayin da ake jiran sauraron buƙatarsa ta beli
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Samaila Kaigama, a gidan gyaran hali na Kuje har sai an fara shari'arsa kan zarge-zargen da suka shafi ta'addanci.
Ana zargin Kaigama ne da zama wakilin ƙungiyar ta'addanci ta ISWAP a tattaunawar neman kudin fansar mutanen da aka yi garkuwa da su.

Source: Getty Images
The Cable ta ruwaito vewa Mai shari'a Ibrahim Salim, wanda ke jagorantar shari'ar, ya bayar da umarnin a ranar Talata bayan Kaigama ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa da su.
Kotu ta dage zaman shari'ar Kaigama
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ce ta gurfanar da shi gaban babbar kotun tarayya tare da shigar da tuhume-tuhume bakwai a kansa.
Alƙalin ya sanya ranar 13 ga Nuwamba domin fara shari'ar, tare da umartar a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma har sai an saurari buƙatarsa ta beli.
Oyedepo Rotimi, daraktan masu gabatar da ƙara na tarayya, ne ya jagoranci tawagar masu gabatar da ƙara, yayin da Chris Abengowe ya wakilci Kaigama.
A yayin zaman kotun, Rotimi ya nemi a tsare Kaigama a gidan gyaran hali na Kuje tare da gaggauta fara shari'ar, kamar yadda TVC News ta rahoto.
Sai dai ƙoƙarin Abengowe na gabatar da hujjojin neman belin wanda yake karewa bai yi nasara ba, saboda buƙatar belin ta dogara ne kan tuhume-tuhumen da kotu ta soke.
Rotimi ya kuma sanar da kotun cewa masu gabatar da ƙara za su shigar da takardar rantsuwa ta mayar da martani domin adawa da buƙatar belin.

Kara karanta wannan
Ribadu ya fadi yadda 'yan ta'adda ke aiki da AI da Kirifto su tara kudi da kai hari
Zarge-zargen da ake yi wa Kaigama
A cikin tuhume-tuhumen da aka gyara, Rotimi ya zargi Kaigama da taimaka wa ayyukan Boko Haram/ISWAP ta hanyar kafa wata hanyar sadarwa ba bisa ƙa'ida ba da mambobin ƙungiyar, tare da shiga tattaunawar biyan kuɗin fansa.
Ana kuma zarginsa da karɓar kuɗin fansa daga iyalan mutanen da aka sace, duk da cewa ana zargin yana da dalilan da za su sa ya yi zaton za a yi amfani da kuɗin wajen ɗaukar nauyin ta'addanci.
Lauyan masu gabatar da ƙara ya ce Kaigama ya gaza bada bayanan da ya sani game da ayyukan yan ta'adda, waɗanda za su iya taimaka wa jami'an tsaro wajen cafke mambobin ƙungiyar da gurfanar da su a gaban kotu.

Source: Twitter
Tuhume-tuhumen sun kuma zargi Kaigama da neman kuɗi da tattara gudummawar kuɗi daga iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su, domin miƙa wa 'yan ta'addan.
A tuhume-tuhumen, ana zargin Kaigama ya yi amfani da manhajar WhatsApp, ta wata ƙungiya mai suna BOSYA, da kuma Facebook wajen neman kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka sace.
Sumayya ta amsa laifin alaka da ISWAP
Kun ji cewa wata mata mai suna, Sumaiya Abubakar ta amsa laifin taimaka wa ’yan ta'addan ISWAP ta hanyar ajiye musu makamai da alburusai a jihar Nasarawa.
Sumaiya ta amsa laifin ne a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja , bayan gwamnatin tarayya ta gurfanar da ita kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi ta’addanci.
Asali: Legit.ng

