Kotu Ta Yi Hukunci bayan Gwamnatin Tarayya Ta Canza Shawara kan Shugaban Hukumar Bogi

Kotu Ta Yi Hukunci bayan Gwamnatin Tarayya Ta Canza Shawara kan Shugaban Hukumar Bogi

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke tuhume-tuhume takwas da ake yi wa shugaban PFIPC ta bogi, Adeniyi Adeyemi bisa buƙatar gwamnatin tarayya.
  • Gwamnatin ta ce binciken fayil ɗin shari’ar ya gano wasu giɓi, tare da cewa Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) ce ta dace ta saurari shari’ar.
  • Ana shirin gurfanar da Adeyemi a gaban Babbar Kotun Abuja kan zargin ƙirƙirar takardun bogi da amfani da hukumar bogi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeira - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kori karar da gwamnatin tarayya ta shigar gabanta kan shugaban hukumar bogi da ake ta ce-ce-ku-ce a kanta, Orince Adeniyi Adeyemi.

Kotun ta soke tuhume-tuhume takwas da gwamnatin tarayya ta shigar kan Adeyemi, wanda ake zargin ya yi ƙarya cewa shi ne Shugaban Hukumar Bunƙasa Sa Hannun Jari daga Ƙasashen Waje ta Fadar Shugaban Ƙasa (PFIPC).

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya rasu, an ɗauke gawarsa daga Abuja

Adeyemi.
Shigaba hukumar bogi ta PFIPC, Prince Adeniyi Adeyemi Hoto: @DejiAdesogan
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai shari’a Mohammed Umar na babbar kotun tarayya ya dakatar da shari’ar Adeyemi a gabansa ne bayan gwamnatin tarayya ta nemi hakan.

Dalilin korar karar a kotun tarayya

Bayanai sun nuna cewa gwamnatin tarayyya karkahsin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta nemi dakatar da shir'ar ne bisa dalilin cewa za a mayar da wanda ake zargin zuwa Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) domin sake gurfanar da shi.

Tun farko dai hukumomin Najeriya sun kama Adeyemi ne kan zargin kirkirar hukumar bogi, jabun takardu da karyar nada shi a matsayin shugaban wannan hukuma.

Wannan lamarin kafa hukumar bogi ya dauki hankalin Najeriya musamman zargin hannun shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, wanda bincike ya nuna ba hannunsa.

Gwamnatin tarayya ta canza tunani

A zaman kotun na ranar Litinin da ta gabata, Rotimi Oyedepo, Babban Lauyan Najeriya (SAN) kuma Daraktan Masu Gabatar da Ƙara na Tarayya (DPPF), ne ya gabatar da buƙatar soke tuhume-tuhumen.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan buƙatar bada belin Nasir El Rufai

Oyedepo ya shaida wa alƙalin cewa Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a (AGF) ya sake nazarin fayil ɗin shari’ar Adeyemi da kuma tuhumar da Sufeto Janar na ’Yan Sanda ya shigar, inda aka gano wasu giɓi.

Adeyemi.
Shugaban hukumar bogi, Prince Adeniyi Adeyemi lokacin da ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya Hoto: Okoduwa Solomon
Source: Twitter

Ya ce daga cikin abubuwan da aka gano, takardun da ake zargin Adeyemi ya ƙirƙira ta hanyar jabu yayin gudanar da ayyukan hukumar boginsa, laifuffuka ne da Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya ce za ta iya saurara, ba Babbar Kotun Tarayya ba.

Wannan dalilin ne ya sa lauyan gwamnati ya nemi dakatar da shari'ar a babbar kotun tarayya, wanda alkalin ta amince da hakan nan take, cewar rahoton Vanguard.

ICPC ta wanke Femi Gbajabiamila

A wani labarin, kun ji cewa ICPC ta kammala binciken ta game da zargin Femi Gbajabiamila da nadin Adeniyi Adeyemi a matsayin shugaban wata hukumar bogi

Binciken ya nuna cewa Adeyemi ne ya ƙirƙiri takardar nadin kansa tare da amfani da takardar aiki ta fadar shugaban ƙasa da sa hannun Gbajabiamila.

ICPC ta ce babu alakar Gbajabiamila da naɗa Adeniyi Adeyemi a matsayin Darakta-Janar na hukumar bogi ta PFIPC da aka kirkira ta haramtacciyar hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262