TikTok Ya Daina Aiki a Kano da Wasu Jihohin Arewacin Najeriya? Bayanai Sun Fito

TikTok Ya Daina Aiki a Kano da Wasu Jihohin Arewacin Najeriya? Bayanai Sun Fito

  • Kamfanin sada zumunta na TikTok ya bayyana ya musanta rade-radin cewa ya daina aiki ko takait amfani da manhajarsa a Arewacin Najeriya
  • Kamfanin ya ce yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin magance matsalolin shiga manhajar da aka ruwaito yan Arewa na fama da shi
  • Ƙungiyoyin fararen hula sun buƙaci gudanar da bincike mai zaman kansa kan matsalar da masu amfani da TikTok suka fuskanta a wasu jihohin Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kamfanin TikTok ya ce musanta takaita amfani da manhajarsa a yankunan Arewacin Najeriya, yana mai cewa rahotannin da ake yada wa ba gaskiya ba ne.

Wannan na zuwa ne yayinda wasu rahotannin da ke cewa masu amfani da TikTok na fuskantar matsalolin shiga manhajar a wasu yankunan Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Ku cire rai kan dawo da tallafin mai': Ƴar takarar shugaban ƙasa ta zare idanu

TikTok.
Dandalin sada zumunta ta TikTok da ake rade radin ta daina aiki a Arewa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Vanguard ta ruwaito cewa Shugabar Sashen Sadarwa na TikTok a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara, Keagile Makgoba, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Litinin.

Kamfanin TikTok ya yi magana

Makgoba ta ce kamfanin na tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samo mafita ga matsalolin shiga manhajar da aka ruwaito mutane na samu a wasu jihohin Arewa.

Ta ce:

“Za mu iya tabbatar da cewa TikTok ba ita ce ta aiwatar da wannan doka ta takaita amfani da manhajar ba, labarin da ke yadawa ba gaskiya be ne.”

Kara karanta wannan

Jarumin Kannywood Adam Zango ba lafiya, mutane na ta masa addu'o'i

Makgoba ta ƙara da cewa kamfanin ya ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa al’ummomin da ke amfani da manhajarsa sun samu damar shiga ta ba tare da wata matsala ba.

Yadda aka fara korafi kan TikTok a Arewa

Tun da farko, an ruwaito cewa wata ƙungiyar haɗin gwiwa ta ƙungiyoyin fararen hula ta buƙaci gudanar da bincike mai zaman kansa kan rahotannin katsewar ko tangardar amfani da TikTok a wasu sassan Arewacin Najeriya.

Ƙungiyoyin sun ce masu amfani da manhajar TikTok a jihohin Kaduna, Kebbi, Kano da Sokoto sun fuskanci matsalolin ɗora bidiyo, kallon abubuwan da aka wallafa da kuma ɗora na su bayanai tun ranar 14 ga Satumba, 2026.

TikTok.
Manhajar sada zumunta ta TikTok a cikin wata wayar hannu Hoto: TikTok
Source: Getty Images

Sun buƙaci hukumomin da abin ya shafa da kamfanonin sadarwa da su binciki musabbabin matsalar, tare da bayyana wa jama’a ko wata umarni ce ta jawo ta ko kuma matsalar fasaha ce.

Hakan ya sa wasu suka fara yada labarin cewa TikTok ya daina aiki a wadannana yakuka, lamarin da kamfanin ya fito ya karyata, yana mai jaddada kudirinsa na gano matsalar da magance ta.

Kara karanta wannan

An hango Shettima a gona a kasar Habasha, ya fadi alherin da zai kawo Najeriya

An kai karar TikTok gaban kotu

A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar Digital Justice ta kai TikTok ƙara a Babbar Kotun Tarayya kan zargin takaita masu amfani da manhajar a wasu jihohin Arewa.

Ta hannun lauyanta, Festus Ogun , ƙungiyar ta roƙi kotu ta tantance ko takunkumin ya tauye ’yancin fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Mai ƙarar ya ce TikTok ba ta da ikon doka na takaita masu amfani a jihohin Arewa, yayin da sauran sassan ƙasar ke samun damar amfani da manhajar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262