Jarumin Kannywood Adam Zango ba Lafiya, Mutane na Ta Masa Addu'o'i
- Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya sanar da cewa zai yi hutun wata uku saboda wasu matsalolin rashin lafiya da yake fama da su
- Jarumin ya ce hutun zai fara ne daga 10 ga Nuwamba, 2026, zuwa 10 ga Fabrairu, 2027, domin samun cikakken hutu da kulawar lafiya
- Magoya bayansa sun cika sashen sharhin sakonsa na Instagram da addu’o’in samun lafiya, yayin da wasu suka bukace shi da ya ba jikinsa isasshen lokacin murmurewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya sanar da cewa zai dakatar da harkokinsa na tsawon wata uku domin kula da lafiyarsa.
Jarumin ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa, inda ya nemi abokan sana’arsa da sauran masoyansa su fahimci halin da yake ciki tare da ba shi goyon baya a wannan lokaci.

Source: Facebook
Sanarwar ta jawo martani daga mabiyansa a Instagram, inda da dama suka yi masa addu’ar samun lafiya da murmurewa cikin gaggawa.
Zango zai tafi hutu
A cikin sanarwar, Zango ya ce wasu matsalolin rashin lafiya da yake fama da su ne suka sa ya yanke shawarar yin hutun, domin samun cikakken hutu da kulawar lafiya.
Ya bayyana cewa zai fara hutun ne a ranar 10 ga Nuwamba, 2026, sannan ya kare a ranar 10 ga Fabrairu, 2027.
Jarumin ya kuma bukaci abokan sana’arsa da su fahimci halin da yake ciki, tare da ba shi hadin kai da goyon baya a lokacin hutun.
Ya kammala sanarwar da rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi lafiya mai dorewa, tare da sanya hutun ya zama sanadin samun sauki da waraka.
Abin da mutane suka fada
Bayan wallafa sanarwar, masu bibiyar shafinsa sun yi ta rubuta sakonnin fatan alheri da addu’o’i a karkashin sakon.

Kara karanta wannan
Bayan rage farashi, Gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan yiwuwar dawo da tallafin fetur kafin 2027
Mai amfani da sunan @lawanahmad ya rubuta cewa,
“Allah ya ba ka lafiya, Amin,”
Yayin da @abba_zaky ya yi masa addu’ar samun lafiya.
Haka kuma, @official_ameena20 ta rubuta cewa:
“Allah ya ba ka lafiya, Baba,”
Yayin da @da_ddy7975 ya roki Allah Ya ba jarumin lafiya.
A nasa bangaren, @shehun_tiktok ya yi addu’ar Allah Ya sa rashin lafiyar ta zama kaffara, sannan Ya ba Zango lafiya mai dorewa.
Shi ma @baballehayatu ya bayyana fatansa na samun sauki ga jarumin, yana mai cewa addu’o’insu za su kasance tare da shi.

Source: Facebook
An bukaci ya kara hutawa
Baya ga addu’o’in samun lafiya, wasu daga cikin masu sharhi sun bayyana cewa jarumin yana bukatar isasshen hutu domin jikinsa ya samu damar murmurewa.
Mai amfani da sunan @abba_zaky ya ce a baya ya taba ganin cewa Zango bai kamata ya dawo aiki da wuri ba, yana mai cewa ya kamata ya kara hutawa domin jikinsa ya samu cikakkiyar sauki.
Haka kuma, @abba_a_dorayi ya yi masa addu’ar Allah Ya ba shi lafiya, yana mai goyon bayan matakin da jarumin ya dauka na tafiya hutu.
A wani sakon kuma, @djamilou8339 ya bayyana cewa za su yi kewar Zango, tare da rokon Allah Ya ba shi lafiya mai amfani.
Yayin da @realshuushuu ta yi masa fatan samun sauki nan ba da jimawa ba, ta kuma roki Allah Ya saukaka masa duk abin da yake damunsa, Ya kuma dawo masa da karfinsa.
Jacob Zuma ba shi da lafiya
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya shiga cikin yanayin da ba a fayyace ba dangane da lafiyarsa.
Rahotannin sun nuna cewa wasu daga cikin iyalansa sun saba da bayanin da jam’iyyar MK ta fitar kan halin da yake ciki.
Wasu bayanai sun ce an kai Zuma, mai shekaru 84, asibiti a ranar Talata bayan ya fara jin rashin lafiya yayin wani gangamin siyasa a lardin KwaZulu-Natal.
Asali: Legit.ng

