Rundunar Yan Sanda Ta Haramta wa Jami’anta Yin Facebook, TikTok
- Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, ya haramta wa jami’an ‘yan sanda amfani da kafafen sada zumunta
- Sabuwar dokar ta hana jami’ai wallafa bidiyo, hotuna ko shirye-shirye cikin kayan aiki na ‘yan sanda ba tare da izini ba
- Disu ya gargadi jami'an cewa karya doka zai fuskanci dakatarwa, rage mukami, hana albashi har zuwa kora daga aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya ba da umarni ga jami'an rundunar kan Facebook da TikTok.
Disu ya haramta wa jami’an ‘yan sanda yin amfani da shafukan sada zumunta. musamman domin samun kudaden shiga.

Source: Twitter
An hana yan sanda amfani da Facebook, TikTok
Premium Times ta ce dokar ta shafi kafafen TikTok, Facebook, Instagram da YouTube wanda zai iya jawo masu matsala.
Sanarwar ta ce dokar ta fayyace kafofin ne musamman idan jami’in ya bayyana kansa a matsayin ma’aikacin rundunar ‘yan sanda.
An bayyana yadda yawaitar kirkirar bidiyoyi da wasu jami’ai ke yi a kafafen sada zumunta ke iya bata martabar rundunar.
Dokar ta hana jami’ai daukar ko wallafa bidiyo, hotuna, barkwanci ko shirye-shirye kai tsaye cikin kayan ‘yan sanda ba tare da izini ba.
Haka kuma an hana jami’ai amfani da asusun sada zumunta na sirri ko na boye domin talla ko kasuwanci saboda matsayinsu.
Dokar ta kuma hana jami’an yin sharhi a bainar jama’a kan binciken ‘yan sanda, ladabtarwa, sauya wurin aiki ko wasu harkokin hukuma.

Source: Twitter
Abubuwan da aka haramta wa yan sanda
Rilwan Disu ya ce jami’ai ba za su karbi tallafi, yarjejeniyar talla ko wata hanya ta samun kudi daga amfani da sunan ‘yan sanda ba.
A cewarsa, rundunar ‘yan sanda cibiya ce mai bin doka, kuma nasararta tana dogara ne da amincewar jama’a da kwarewar jami’ai.
Ya gargadi cewa masu karya wannan doka na iya fuskantar dakatarwa daga aiki, rasa albashi, rage mukami ko kora daga aiki.

Kara karanta wannan
Wani bam da aka dasa a cikin mota ya tashi a wurin hada hadar kasuwanci a jihar Legas
Idan laifin ya shafi dokokin laifuffuka ko na yanar gizo, jami’in na iya fuskantar gurfanarwa a gaban kotu, cewar Sahara Reporters.
Dokar ta kuma dorawa kwamishinonin ‘yan sanda da sauran manyan jami’ai alhakin sa ido da ladabtar da masu karya umarnin.
An umurci kwamishinonin jihohi su sanar da dukkan jami’ansu cikin kwanaki bakwai tare da aika rahoton bin umarni cikin kwanaki 14.
Wannan mataki ya zo ne kasa da wata guda bayan Disu ya gargadi jama’a da masu kirkirar bidiyo kan yada bidiyon ‘yan sanda ba tare da cikakken bayani ba.
Ya bayyana cewa yada tsofaffin bidiyoyi ko wadanda aka sauya na iya haddasa firgici tare da kawo cikas ga kokarin tabbatar da tsaro.
Kisan mata: 'Yan sanda sun cafke mutane 24
An ji cewa rundunar ‘yan sandan Kaduna ta cafke wasu mutane 24 da ake zargi da hannu wajen kashe wa da kona gawar wata mata a Maraban Jos.
An tabbatar da cewa na gurfanar da su ne a kotun majistare inda ta ba da umarnin tsare wadanda ake zargin a gidan gyaran hali.
'Yan sanda sun ce sama da mutum 100 na ci gaba da fuskantar bincike kan zargin hannu a wannan mummunan danyen aiki a Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
