Dalilin da Ya Sa Sojoji Suka Cafke Babban Dan Siyasa kan Zargin Taimakon 'Yan Ta'adda
- Dakarun Operation Hadin Kai sun kama Wakil Goni Mama, wanda aka fi sani da Mai Salati, bisa zargin taimaka wa Boko Haram da ISWAP
- Majiyoyin sojoji sun yi zargin cewa ya yi ƙoƙarin ba sojoji kuɗi domin sakin waɗanda aka kama a Kanamma, Jihar Yobe
- Ƙungiyar Yobe Network Against Violent Extremism ta buƙaci jama’a da ’yan siyasa su guji siyasantar da lamarin, tare da barin bincike ya gudana bisa doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Yobe - An samu sababbin bayanai kan kama fitaccen ɗan siyasa a jiihar Yobe, Wakil Goni Mama, wanda aka fi sani da Mai Salati.
Ana zargin dan siyasar da samar da tallafin kayayyaki da dabaru ga ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP da ke aiki a Arewa maso Gabas.

Source: Facebook
Me yasa sojoji suka cafke Mai Salati?

Kara karanta wannan
Jita jita ta ƙare, an fito da bayanin da ya kamata mutane su sani kan hatsarin jirgin sojoji
Zagazola Makama ya ruwaito cewa dakarun Operation HADIN KAI sun kama shi ranar Asabar, bayan samun bayanan sirri da majiyoyin soji suka bayyana a matsayin sahihai, waɗanda suka danganta shi da mutanen da ake zargin suna taimaka wa ’yan ta’adda.
Kamen da aka yi wa Mai Salati ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke zargin cewa akwai katsalandan na siyasa a lamarin.
Sai dai wasu majiyoyi da suka san yadda aikin ya gudana, waɗanda suka yi magana da jaridar Daily Nigerian ba tare da bayyana sunayensu ba, sun ce an kama ɗan siyasar ne bisa zargin taimaka wa Boko Haram da ISWAP da ke yankin.
Zargin ƙoƙarin ba sojoji kuɗi
Majiyoyin sun ce kamen ya biyo bayan zargin cewa Mai Salati ya yi ƙoƙarin ba jami’an soji cin hanci domin a saki wasu mutanen da aka kama a Kanamma, Jihar Yobe.
A cewarsu, kamen ya kasance ƙarshen wani dogon aiki na tattara bayanan sirri da kwamandan Sector 2 da rundunar 27 Task Force Brigade suka jagoranta domin gano shi da kama shi.
Majiyoyin sun zargi ɗan siyasar da kasancewa babban mai samar da kayayyaki da tallafi ga ’yan ta’addan.
Sun ce ana shirya waɗanda aka kama a Kanamma domin ci gaba da bincike lokacin da Mai Salati ya yi ƙoƙarin shiga tsakani ta hanyar miƙa kuɗi ga sojoji domin a sake su.
Rahoton ya ce sojojin sun ƙi karɓar kuɗin, suka kama shi, sannan suka fara shirye-shiryen miƙa shi Maiduguri domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar ɗaukar matakin shari’a.
Jaridar ta kuma ce ta ga wani faifan bidiyo da ake zargin yana nuna ɗan siyasar yana ƙoƙarin ba jami’an soji kuɗi dangane da ƙoƙarin sakin mutanen da aka kama.
Ƙungiya ta buƙaci a guji siyasantar da binciken
Ƙungiyar Yobe Network Against Violent Extremism ta yi kira ga jama’a da ’yan siyasa da su bar hukumomin tsaro su kammala binciken lamarin Mai Salati, tare da guje wa mayar da zarge-zargen ta’addanci batun siyasa.
A cikin sanarwar da shugabanta, Ibrahim Goni, ya fitar, ƙungiyar ta ce jita-jita da bayanan da aka gauraya da siyasa a kafafen sada zumunta na iya karkatar da hankalin jami’an tsaro daga aikinsu.
Ta tuna cewa yankin Arewa maso Gabas ya sha fama da ta’addanci, gudun hijira da lalacewar kadarori tsawon shekaru. Dubban iyalai sun fuskanci matsaloli, yayin da jami’an tsaro da dama suka sadaukar da rayukansu wajen kare al’umma.
Ƙungiyar ta ce dole ne a binciki duk wani sahihin zargi da ya shafi samar da kuɗi ko kayayyaki ga ’yan ta’adda, taimaka musu, ɗaukar mayaƙa, ɓoye su ko ba su wani tallafi, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ko matsayin wanda ake zargi ba.

Kara karanta wannan
An ga tashin hankali da 'yan ta'adda suka hallaka sojoji da dan kasar waje a Kebbi

Source: Original
Sojoji sun gano bama-bamai
A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin Operation Fansan Yamma sun gano tare da lalata bama-bamai biyu da ake zargin ’yan ta’adda sun dasa a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Dakarun sojojin sun samu nasarar kwance bama-baman ne a kan titin Magami-Hannutara-Dansadau da ke Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Asali: Legit.ng