Sojoji Sun Gano Bama Bamai 2 da Yan Bindiga Suka Dasa domin Kashe Bayin Allah

Sojoji Sun Gano Bama Bamai 2 da Yan Bindiga Suka Dasa domin Kashe Bayin Allah

  • Sojoji sun gano tare da lalata bama-bamai biyu da ake zargin ’yan ta’adda sun dasa a hanyar Magami-Hannutara-Dansadau da ke jihar Zamfara
  • Sojojin sun gano bama-baman ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan barazanar da suke yi wa matafiya masu amfani da hanyar
  • Rundunar sojin ta ƙara yawan sintiri da sa ido a yankin, tare da buƙatar jama’a su kai rahoton duk wani abu ko motsi da suke zargi ga jami’an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon.shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Sojojin Operation Fansan Yamma sun gano tare da lalata bama-bamai biyu da ake zargin ’yan ta’adda sun dasa a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Dakarun sojojin sun samu nasarar kwance bama-baman ne a kan titin Magami-Hannutara-Dansadau da ke Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

Soja.
Wani jami'in sashen ganowa da kwance bama-bamai a lokacin da yake kokarin lalata wanai bam a titin Zamfara Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma (OPFY) ta fitar wacce aka wallafa a shafin rundunar sojin kasa na Facebook.

Kara karanta wannan

Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take

Sanarwar ta bayyana cewa an gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan barazanar bama-bamai da yan ta'adda suka yi wa matafiya da ke amfani da hanyar.

Yadda sojoji suka gano bama-bamai

Sojojin Sashe na Biyu na rundunar Operatiom Fansan Yamma sun kewaye yankin da abin ya shafa tare da gudanar da bincike, inda suka gano wurare biyu da aka dasa bama-baman.

Daga nan ne aka tura tawagar kwararru kan gano da kuma kawar da bama-bamai domin gudanar da aikin.

Tawagar ta lalata bam guda ɗaya, yayin da ta gano ɗayan kuma ta kwance haɗarinsa cikin aminci, lamarin da ya hana aukuwar wani mummunan haɗari ga masu amfani da hanyar.

An kara tsaurara matakan tsaro

Rundunar ta ce tun bayan wannan aiki, dakarun sojoji sun ƙara yawan sintiri da sa ido a yankin domin kare mazauna da kuma hana sake samun irin waɗannan barazanar.

Kara karanta wannan

Jirgin saman Najeriya ya yi saukar gaggawa a gona bayan hadarin jirgi a Ondo

Sojojin sun kuma buƙaci jama’a da su kasance cikin shiri tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi ko motsin da ba a saba gani ba ga ofishin hukumar tsaro mafi kusa cikin gaggawa.

Sojoji.
Sojoji lokacin da suka dauko daya daga cikin bama-baman da suka tono a Zamfara Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Wannan dai na zuwa ne yayin da al'ummar jihar Zamfara ke ci gaba da fuskantar matsalar tsaro, wacce ta hada da hare-haren yan bindiga, garkuwa da mutane da sauransu.

An kashe Kachalla Mu'azu a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa an kashe wani fitaccen jagoran ’yan bindiga, Kachalla Mu’azu, da wasu ’yan ƙungiyarsa shida a wani artabu tsakanin ƙungiyoyi yan ta'adda a Zamfara.

Kachalla Mu’azu da mutanensa suna dawowa ne daga Kasuwar Yankara lokacin da mambobin wata dabar ’yan bindiga suka kai musu harin kwanton bauna a kan hanyar da suke bi.

An bayyana Mu’azu a matsayin wani fitaccen kwamandan ’yan bindiga da ake zargi da hannu a ayyukan laifi da hare-haren da suka shafi al’ummomin Gusau da sauran sassan Jihar Zamfara, da wasu yankunan Jihar Katsina .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262