Sojoji Sun Cafke Babban Dan Siyasa a Najeriya kan Taimakon 'Yan Ta'adda
- Dakarun sojin Najeriya sun kama wani ɗan siyasa a jihar Yobe, Alhaji Wakiil Goni Mama, wanda aka fi sani da Mai Salati, kan zargin tallafa wa ’yan ta’addan ISWAP
- Ana zargin ɗan siyasar da ƙoƙarin ba sojoji cin hanci domin su saki wasu mutane da aka kama bisa zargin samar da kayayyakin tallafi ga ’yan ta’adda a Kanamma
- Rahotanni sun ce an kama Mai Salati ne bayan dakarun Operation Hadin Kai sun ƙi karɓar kuɗin da ake zargin ya yi yunƙurin ba su, yayin da aka shirya miƙa shi Maiduguri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Yobe – Dakarun rundunar sojin Najeriya na Operation Hadin Kai sun kama wani ɗan siyasa a jihar Yobe, Alhaji Wakiil Goni Mama, wanda aka fi sani da Mai Salati, bisa zargin tallafa wa ƙungiyar ISWAP.

Kara karanta wannan
Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take
Rahoto ya nuna cewa majiyoyin tsaro sun ce an kama ɗan siyasar ne bayan an gano zargin yunƙurinsa na ba sojoji cin hanci domin a saki wasu waɗanda aka kama a Kanamma.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da kama Mai Salati ne a wani sako da mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X.
An kama dan siyasa Mai Salati
Majiyoyin tsaro sun ce kama ɗan siyasar ya biyo bayan binciken sirri da dakarun rundunar 27 Task Force Brigade suka gudanar.
Rahoton ya bayyana cewa sojoji sun kama wasu mutane a Kanamma bisa zargin hannu wajen samar da kayayyakin tallafi ga ’yan ta’adda, kuma ana gudanar da bincike a kansu lokacin da Mai Salati ya yi yunƙurin shiga tsakani domin a sake su.
Ana zargin ɗan siyasar da ƙoƙarin ba sojojin kuɗi domin su saki mutanen, amma maimakon karɓar kuɗin, dakarun sun kama shi tare da fara shirye-shiryen miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike.
An kai Mai Salati Borno
Rahoton ya ce daga bisani an ɗauki Mai Salati da sauran waɗanda aka kama daga Damaturu zuwa Maiduguri domin yi masu tambayoyi da gudanar da cikakken bincike.
The Cable ta wallafa cewa hukumomin tsaro na ƙoƙarin gano ko akwai alaƙa tsakanin mutanen da aka kama da ƙungiyoyin ta’addanci, da kuma irin gudunmawar da ake zargin sun bayar wajen taimaka wa ayyukansu.
Sai dai har yanzu zarge-zargen da ake yi wa Mai Salati suna buƙatar tabbatarwa ta hanyar bincike da kuma shari’a. Ba a tabbatar da laifinsa a kotu ba.
Mai Salati dan ADC ne
Rahoton ya kuma ce lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu suka yi zargin cewa kama Mai Salati yana da alaƙa da siyasa, musamman batun sauya sheƙarsa daga jam’iyyar APC zuwa ADC.
Sai dai majiyoyin tsaro sun musanta wannan ikirari, suna masu cewa matakin ya shafi zargin tallafa wa ’yan ta’adda da yunƙurin hana gudanar da bincike kan mutanen da ake zargin suna samar wa ISWAP kayayyakin tallafi.

Source: Original
Za a rataye 'yan fashi a Gombe
A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Jihar Gombe ta yanke wa wasu mutane biyu, Buhari Sule da Muktari Ali Hilami, hukuncin kisa ta hanyar rataya kan fashi da makami.
Alƙali Muhammad-Auwal Haruna ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba, bayan kotun ta same su da laifin haɗa baki wajen aikata laifi, fashi da makami da kuma kisan kai.
Lamarin ya shafi harin da aka kai wa Rabi’u a ƙauyen Garin Galadima da ke kusa da Pindiga, a ƙaramar hukumar Akko ta Gombe, ranar 18 ga Satumba, 2025.
Asali: Legit.ng

