Jita Jita Ta Kare, An Fito da Bayanin da Ya Kamata Mutane Su Sani kan Hatsarin Jirgin Sojoji

Jita Jita Ta Kare, An Fito da Bayanin da Ya Kamata Mutane Su Sani kan Hatsarin Jirgin Sojoji

  • Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta tabbatar da cewa mutane 25 ne ke cikin jirgin ATR 42 da ya yi hatsari a Igbokoda, Jihar Ondo
  • Mutanen sun haɗa da fasinjoji 20 da ma’aikatan jirgin biyar, yayin da aka ƙirga wasu ma’aikata biyu da ba sa bakin aiki a cikin fasinjojin
  • NAF ta ce ana ci gaba da bincike kan musabbabin hatsarin, tare da ba iyalan waɗanda suka rasu tallafin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ƙara fayyace rahotannin da suka shafi adadin mutanen da ke cikin jirginta samfurin ATR 42 mai lamba NAF 931, wanda ya yi hatsari a ranar Litinin a Igbokoda, Jihar Ondo.

Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ne ya yi wannan ƙarin bayani a wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar a Abuja.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa har cikin harabar cibiyar CRIN ta Najeriya, sun sace ma'aikata

Wurin hadarin jirgi.
Wurin da jirgin sojojin Najeriya ya yi hatsari a jihar Ondo Hoto: @zagazolamakama
Source: Facebook

A rahoton Vanguard, Ejodame ya ce bayanai sun tabbatar da cewa mutane 25 ne ke cikin jirgin, waɗanda suka haɗa da fasinjoji 20 da ma’aikatan jirgin biyar da ke bakin aiki.

Ya ƙara da cewa an haɗa wasu ma’aikatan jirgin biyu da ba sa bakin aiki cikin fasinjoji 20 ɗin.

Rundunar sojin sama ta yi bayani

Ya ce rahotannin da suka ambaci mutane 32 ne a cikin jirgin sun samo asali ne daga rashin fahimtar kalmomin fasahar zirga-zirgar jiragen sama, kamar furucin “mutane 25 a cikin jirgin, ciki har da ma’aikata bakwai”.

A cewarsa, wannan furuci na nufin mutane 25 ne gaba ɗaya, daga cikinsu ne har da ma’aikatan jirgin bakwai, ba wai fasinjoji 25 ban da ma’aikatan jirgin bakwai ba.

Dangane da fararen hular da ke cikin jirgin, Ejodame ya ce ’yan uwa ne na wasu jami’an rundunar da suke tafiya zuwa wuri ɗaya.

Kara karanta wannan

Bayan fetur, Gwamnatin tarayya na shirin rage hauhawar farashin muhimman kayayyaki

Ya ce NAF ta fitar da adadin mutanen da aka tabbatar da kasancewarsu a cikin jirgin da kuma sunayensu bayan gudanar da ayyukan bincike da gano gawarwaki, tare da tattaunawa da iyalan waɗanda lamarin ya shafa.

NAF ta godewa masu nuna alhini

A cewarsa, duk da ci gaba da alhinin wannan mummunan rashi, rundunar tana matuƙar godiya ga ’yan Najeriya da sauran masu fatan alheri bisa ta’aziyya, goyon baya da nuna haɗin kai da suka yi.

“Waɗannan saƙonnin nuna damuwa sun kasance wata hanya ta samun ta’aziyya a wannan lokaci mai wahala.
“Waɗanda muka rasa ba adadin waɗanda suka mutu kawai ba ne, rayuka ne masu daraja, mutanen da ake kauna kuma waɗanda rashinsu ya taɓa zuciyar rundunar da ƙasa baki ɗaya,” in ji shi.
Air Marshal Sunday Aneke.
Babban hafsan rundunar sojojin sama ta Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke lokacin da ya je wurin da jirgi ya yi hatsari Hoto: HQ Nigerian Air Force
Source: Facebook

Ejodame ya ce NAF na ci gaba da hulɗa da iyalan waɗanda suka rasu, tare da ba su tallafin da ya dace yayin da suke fuskantar wannan lokaci mai raɗaɗi.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan hatsarin jirgin, inda ya ƙara da cewa za a sanar da ƙarin bayani a lokacin da ya dace, kamar yada The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jirgin saman Najeriya ya yi saukar gaggawa a gona bayan hadarin jirgi a Ondo

Janar Musa ya yi alhinin hadarin jirgi

Kun ji cewa Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana matuƙar jimami kan hatsarin jirgin NAF ATR 42 da ya yi sanadin mutuwar mutane 25.

Musa ya miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shugabannin rundunonin sojin Najeriya da iyalan waɗanda suka rasu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262