'An ga Tashin Hankali da Yan Ta'adda Suka Hallaka Sojoji da Dan Kasar Waje a Kebbi
- ’Yan ta'addan da ake zargin Lakurawa ne sun kashe sojoji biyu da wani ɗan China a harin da suka kai wa ma’aikatan gina hanya Maiyama
- Kakakin rundunar ’yan sandan Kebbi ya ce sojojin na ba da kariya ga ɗan China da sauran ma’aikatan da ke aikin gina hanya
- Jami’an tsaro sun fara farautar waɗanda ake zargi da kai harin, yayin da wasu mutane suka samu raunuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Wasu ’yan ta'adda da ake zargin ’yan kungiyar Lakurawa ne sun kashe sojoji biyu da wani ɗan China a wani hari da suka kai wa ma’aikatan gina hanya a jihar Kebbi.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoban 2026 a ƙaramar hukumar Maiyama, lokacin da maharan suka kai wa ma’aikatan hari ba zato ba tsammani.

Kara karanta wannan
INEC ta raba gardama, ta fadi matakin dauka kan jam'iyyun da suka karya dokar zabe

Source: Original
Rahoton jaridar Leadership ya ce ana zargin maharan sun shiga jihar Kebbi ne ta ƙaramar hukumar Kebbe da ke makwabtaka da ita a jihar Sokoto.
An kai harin kan ma’aikatan gina hanya
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce waɗanda aka kashe na cikin ma’aikatan da ke aikin gina hanyar Badagry Super Highway a jihar.
A cewarsa, sojojin biyu na aikin ba da kariya ga ɗan China da sauran ma’aikatan lokacin da maharan suka kai harin.
SP Bashir Usman ya ce:
“Eh, an kai harin, amma ’yan ta’addan ba daga jihar Kebbi suke ba. Sun shiga jihar ne ta wani ƙauye da ke kan iyakar Kebbi.”
Ya ƙara da cewa maharan sun kashe sojojin biyu da ɗan China, yayin da wasu mutane da dama suka samu raunuka.
’Yan sanda sun ce ba za su bayyana sunayen sojojin ba
Kakakin ’yan sandan ya ce ba za su iya bayyana sunayen sojojin da aka kashe ba, saboda ba jami’an rundunar ’yan sanda ba ne.
"Ba za mu iya ba ku sunayen waɗanda aka kashe a harin ba, domin ba jami’an ’yan sanda ba ne.” In ji shi.
Jami’an tsaro sun fara farautar maharan
Usman ya bayyana harin a matsayin abin takaici da rashin dalili, tare da tabbatar da cewa jami’an tsaro sun fara ƙoƙarin gano waɗanda suka aikata shi, Channels tv ta kawo rahoton.
"Haɗin gwiwar jami’an tsaro na bin sawun waɗanda ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne, waɗanda suka kai harin suka kashe sojoji biyu da wani ɗan China.” In ji shi.
Ana ci gaba da ƙoƙarin gano maharan da kuma tabbatar da cikakken bayani kan waɗanda suka jikkata a harin.

Source: Twitter
Sojoji sun dakile harin 'yan ISWAP
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun bataliya ta 101 ta musamman ta sojojin Najeriya da ke Kukawa, Jihar Borno, sun yi nasarar fatattakar wani babban hari da ’yan ta’addan ISWAP suka kai sansaninsu.
Majiyoyin tsaro sun ce ’yan ta’addan sun kai harin ne daga wurare huɗu daban-daban, a wani yunƙuri na mamaye sansanin sojojin.
Asali: Legit.ng
