Yan Bindiga Sun Shiga Gari a lokacin da Mutane ke Hutun Yamma, Sun Bude Wuta

Yan Bindiga Sun Shiga Gari a lokacin da Mutane ke Hutun Yamma, Sun Bude Wuta

  • An kashe aƙalla mutane uku, ciki har da yaro mai shekaru uku, a wani hari da ake zargin makiyaya masu ɗauke da makamai sun kai a jihar Benue
  • Maharan sun kai hari kan al’ummar kauyen Omulonye da ke Ugboju Icho, a ƙaramar hukumar Otukpo, a yammacin ranar Laraba
  • Rundunar ’yan sandan jihar Benue ta tabbatar da mutuwar mutane uku, yayin da wasu mazauna yankin da suka ji rauni ke karɓar magani a Otukpo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue, Nigeria - Wasu yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya masu ɗauke da makamai ne sun kai mummunan hari kan al’ummar kauyen Omulonye da ke Ugboju Icho, a ƙaramar hukumar Otukpo ta jihar Benue.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun kashe aƙalla mazauna yankin uku, ciki har da yaro mai shekaru uku.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Mutane 5 'yan gida 1 sun mutu daga kamuwa da cuta a Kano

Gwamna Alia.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Lormem Alia yana jawabi ga menam labarai a gidan gwamnatinsa da ke Makurdi Hoto: Rev. Hyacinth Lormem Alia
Source: Facebook

Rahotannin da jaridar Leadership ta samu sun bayyana cewa maharan sun shiga cikin garin ne a yammacin ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba, 2027* inda suka jikkata wasu mazauna yankin da dama.

Yadda aka kashe mutane 3 a Benue

An ruwaito cewa a halin yanzu waɗanda suka ji raunin a harin suna kwance suna karɓar magani a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba a garin Otukpo.

Wani shaidan gani ido, wanda ya zanta da yan jarida bisa sharadin ɓoye sunansa, ya ce wasu makiyaya masu ɗauke da makamai ne suka kai harin.

Mutumin ya kuma yi zargin cewa yan bindigar da suka kai hari sun dade a yankin, kuma ana zargin sun daɗe suna addabar yankin a baya-bayan nan.

“Makiyaya masu ɗauke da makamai da suka daɗe suna addabar yankin sun kashe mutane uku. Ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe yaro ne mai shekaru uku.

Kara karanta wannan

Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take

"Wasu mutanen kuma sun ji rauni kuma yanzu haka dai suna karɓar magani a Otukpo,” in ji shaidan gani idon.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da harin

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benue, DSP Peter Orchia Aondongu, ya tabbatar da aukuwar lamarin yayin da aka tuntube shi.

Aondongu ya bayyana cewa ya ssmu rahoton da ke nuna an kashe mutane uku a wannan harin da aka kai kauyen da ke yankin Ƙaramar Hukumar Otukpo.

“Eh, zan iya tabbatar muku da cewa an kashe mutane uku a ɗaya daga cikin kauyukan da ke karkashin Ugboju, a Ƙaramar Hukumar Otukpo,” in ji shi.
Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: PoliceNG
Source: Twitter

An kashe shugaban NDC a Benue

A wani labarin na daban, kun ji cewa wasu mahara sun kashe shugaban jam'iyyar NDC na mazabar Fiidi da ke yankin Makurdi a jihar Benue da ke Arewa ta Tsakiya, Hon. Igbu Job Terhemen.

An ce wasu ’yan daba ake zargi sun kai wa Terhemen hari da misalin ƙarfe 2:00 na dare, inda suka daure shi da igiyoyi, suka yi masa allurar wani abu da ake zargin mai guba ne.

Wani abokin marigayin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa ’yan jarida a Makurdi cewa Terhemen ya bar gidansa da yammacin Talata domin kallon wasan ƙwallon ƙafa a yankin Kanshio, amma bai dawo gida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262