Yan Bindiga Sun Kutsa har cikin Harabar Cibiyar CRIN Ta Najeriya, Sun Sace Ma'aikata
- ’Yan sanda a jihar Oyo sun tabbatar da sace ma’aikata uku na Cibiyar Binciken Koko ta Najeriya (CRIN) da ke Ibadan
- Yan bindiga sun yi awon gaba da ma’aikatan ne yayin da suke duba amfanin gona a wata gona da ke cikin harabar cibiyar
- ’Yan sanda sun ce sun fara farautar waɗanda suka aikata laifin tare da ƙoƙarin kuɓutar da waɗanda aka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta tabbatar a ranar Juma’a cewa an sace ma’aikata uku na Cibiyar Binciken Koko ta Najeriya (CRIN) da ke Ibadan a jihar Oyo.
Rundunar yan sandan ta kuma tabbatar da cewa ana ƙoƙarin kuɓutar da su cikin ƙoshin lafiya tare da kama waɗanda suka aikata laifin.

Source: Twitter
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Olayinka Ayanlade, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Ibadan, babban birnin jihar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Kakar miliyoyin matasa ta yanke saƙa, an fadada shirin tallafin rage talauci a Najeriya
Rahotanni sun bayyana cewa yan bindiga sun sace ma’aikatan ne yayin da suke duba amfanin gona a wata gona da ke cikin harabar cibiyar.
’Yan NYSC 20 sun kuɓuta a Imo
Wannna na zuwa ne bayan an cetonmutum 20 daga cikin matss 30 da ke shirin shiga aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC), waɗanda aka sace a jihar Imo a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.
An sace su ne yayin da suke tafiya a cikin motocin bas guda biyu daga jihar Oyo zuwa sansanonin horaswa da ke jihar Abia. Sauran mutum 10 sun tsere ta cikin daji.
’Yan sanda sun fara farautar maharan
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, Ayanlade ya ce:
“Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta tabbatar da sace ma’aikata uku na CRIN, waɗanda aka yi garkuwa da su yayin da suke duba amfanin gona a wata gona da ke cikin harabar cibiyar.

Kara karanta wannan
Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take
“Bayan samun rahoton lamarin, rundunar ta fara ɗaukar matakan gaggawa da suka haɗa da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya da kuma kama waɗanda suka aikata laifin.
"An fara farautar waɗanda ake zargi, kuma ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin tabbatar da dawowar waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a lamarin a gaban shari’a."

Source: Facebook
Rundunar ta yi kira ga duk wanda yake da sahihan bayanai da za su taimaka wa aikin da ake gudanarwa da ya gaggauta kai rahoto ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kuma ya tuntubi rundunar ta hanyoyin da aka tanada.
Sojoji sun ceto mutane 16 a Kogi
Kun ji cewa rundunar Sojin Najeriya ta jagoranci wani samame da ya kai ga ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a jihar Kogi.
An gudanar da aikin ceto ne bayan da jami'an tsaro suka samu bayanan sirri kan inda aka kai mutanen da aka sace.
Asali: Legit.ng